NIAMEY, NIGER - Alkaluman hukumomin Nijar sun yi nuni da cewa kashi 50 daga cikin 100 na al’umar kasar a yankunan karkara na fama da rashin ruwan sha ko kuma karancinsa duk kuwa da cewa batun samar da ruwan sha na daga cikin matsalolin da ‘yan siyasa ke shan alwashi akansu a yayin yakin neman zabe.
Saboda haka ne kungiyar REJEA ta hada guiwa da gidauniyar Noor wajen shirya wannan taro da ya hada masu ruwa da tsaki akan maganar albarkatun ruwa don ankarar da su halin da ake ciki.
Samun ruwan sha mai tsafta ‘yanci ne da kundin tsarin mulkin Nijar ya yi tanadi domin jama’ar kasar wacce a wani bangare ta rattaba hannu akan yarjeniyoyin kasa da kasa a wannan fanni mafari kenan aka yi tunatarwa a yayin wannan zama.
Ministan albarkatun ruwa Adamou Mahaman ya jaddada niyyar gwamnatin Nijar wajen karfafa hanyoyin samar da wadatar ruwan sha kafin nan da shekarar 2030 kamar yadda ta kudirta a shekarar 2017 ta hanyar wasu kundayen doka kunshe da tsarin ayyukan inganta wannan fanni.
Domin bin diddigin shawarwarin da aka bayar a wannan taro kungiyar ta REJEA ta nada shugabar gidauniyar Noor wato uwargidan shugaban kasar Nijar Hajiya Hadiza Bazoum a matsayin jakadiyar al’umma mai fafitikar samar da ruwan sha da inganta sha’anin tsafta.
Ta ce ta dauki alkawarin shigar da wadanan bukatu kuma zata tayar da dukkan masu ruwa da tsaki na cikin gida da na waje daga barci domin cimma burin da aka sa gaba a karkashin wannan babbar niyya.
Gudanar da wannan taro a wani lokacin da kasashen duniya ke shirin halartar babban taron ruwan sha da za a fara a ranar 21 ga watan nan na Maris a birnin Dakar na kasar Senegal wata hanya ce ta tattara bayanan da za su janyo hankulan masu hannu da shuni su dauki halin da ake ciki a Nijar da mahimmanci yayinda kuma ake shirin bukin ranar ruwa ta duniya kamar yadda aka saba a ranar 22 ga watan Maris din kowace shekara.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma: