Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Majalisar Dokokin Kasa Mata Sun Gabatar Da Bukatar Gyara a Dokokin Kare Hakkin Mata Da Yara


A jamhuriyar Nijer a karshen wani taron da ya hada sarakunan gargajiya, shugabaninn addinai, wakilan kungiyoyin cikin gida, na MDD, da na kungiyar EU don duba halin da ake ciki game da batun mutunta ‘yancin mata da yara kanana.

Kungiyar mata ‘yan majalisar dokokin kasa ta bukaci goyon bayan hukumomi da ‘yan majalisar dokoki akan maganar kwaskware wasu dokokin da ake ganin ba su dace ba da tafiyar duniya a yau.

Galibin dokokin da Nijer ke amfani da su wajen kare hakkin mata da yara kanana, abubuwa ne da suka samo asali a 1961, wadanda kuma masana suka gano cewa yawancinsu sun yi hannun riga da yanayin zamantakewar al’uma a yau, mafarin kiran wani babban taro da ya zakulo wasu shawarwarin dake kunshe cikin wani kundin musamman da ake fatan ganin majalisar dokokin kasa ta yi na’am da su a matsayin doka.

Dabi’ar cin zarafin mata da yara kanana a kasashe masu tasowa irinsu Nijer abu ne da ya zama ana magani kai ya na kaba, a cewar shugabar ofishin ‘yan sanda mai kare hakkin mata da yara kanana, Commissaire Principale Zouera Haoussaize, lamarin na bukatar kara jan damara.

Kungiyar mata ‘yan majalisa ta damka wannan kundi a hannun babban jam’in shiga Tsakani na kasa Mediateur de la Republique Me Sirfi Maiga wanne shi kuma ya isar da shi a hannun mataimakin kakakin majalisar dokokin kasa Kalla Hankourao.

Ya ce da hadin kan gwamnati za mu yi iya kokarinmu domin samar da ci gaba a yaki da muzugunawa mata da yara. Abu ne da ya zama dole a gare mu saboda mun san da cewa mata da maza tare mu ke rayuwa kuma akwai sauran aiki a wannan fanni, yanzu dai aiki ya rage namu kuma ya rage na bangaren zartarwa.

Majalisar Dinkin Duniya da Tarayyar EU sun taka rawa wajen shirya wannan zama dake matsayin wani bangare na shirin hadin gwiwar da suka kira initiative Spotlight mai hangen kawar da dabi’ar cin zarafin mata da ‘yan mata a doron kasa. Omer Kebiwou KALAMEU, Phd shine wakilin Majalisar Dinkin Duniya a wurin wannan taro.

Ya ce mu a matsayinmu na Majalisar Dinkin Duniya za mu ci gaba da dafawa ma dukkan bangarorin dake cikin wannan tafiya ta yadda Nijer za ta samu sukunin cika alkawuran da ta dauka akan batun mutunta ‘yancin mata da yara kanana. Magana ce ta sauke nauyin da ya rataya a wuyarta.

Daga cikin kujeru 171 na wakilicin al’umma a majalisar dokokin kasa mata na da kujeru 50 a halin yanzu adadin da ake ganin zai iya tasiri wajen ganar da daukacin ‘yan majalisar su amince da wadannan shawarwari na kwaskware dokokin da ake ganin su na haddasa tarnaki ga yaki da dabi’ar cin zarafin mata da yara kanana.

Nan gaba a cikin watan nan na maris ne majalisar za ta yi zamanta na shekara shekara don nazarin kudirorin doka wato session des lois.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti :

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG