Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane Miliyan 27 Na Fuskantar Karancin Abinci A Afurka Ta Yamma


As drought grips the Horn of Africa, an aid worker films the rotting carcass of a cow with in iPad near the Kenya-Somalia border, July 23, 2011. (Reuters)
As drought grips the Horn of Africa, an aid worker films the rotting carcass of a cow with in iPad near the Kenya-Somalia border, July 23, 2011. (Reuters)

Wani rahoton kungiyar oxfam ya ayyana cewa mutane miliyon 27 na fuskantar karancin abinci a kasashen Afurka ta yamma kuma akwai yiwuwar samun karuwar wasu mutane mil

iyon 11 da za su fada cikin irin wannan yanayi sakamakon matsalolin da ake fama da su a yankin muddin ba a gaggauta daukar matakai ba.

Rahoton na kungiyar Oxfam ya nuna cewa an shiga mafi tsananin yanayin karancin abinci da yankin Afurka ta yamma ya tsinci kansa ciki a tsawon shekaru 10 na baya bayan nan, inda matsalolin tsaro da farin da aka fuskanta a damanar da ta gabata suka jefa miliyoyin mutane cikin halin kuncin rayuwa kuma a bisa ga dukkan alamu matsalar na iya ta’azzara.

Jam’in kungiyar AEC, Diori Ibrahim, mai kula da yaki da karancin abinci na danganta faruwar wannan al’amari da halin ko in kular da gwamnatoci ke nunawa ma fannin noma da kiwo.

Wannan al’amari na faruwa a wani lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta aiyana cewa yara ‘yan watanni 6 zuwa shekara 5 kimanin miliyon kusan 7 ne ke cikin halin bukatar abinci mai gina jiki adadin da ya zarta na shekarar da ta gabata abinda ya sa Shugaban kungiyar manoma da makiyaya ta Plate forme Paysanne Djibo Bagna ke ganin bukatar maida hakali wajen noman rani a wadanan kasashe.

Rahoton ya ambato darektar kungiyar Oxfam a yankin Afurka ta Yamma da Afurka ta tsakiya, Assalam Dawalack Sidi, ta na nuna damuwa akan yadda matsalolin fari da na ambaliyar ruwa da tashe tsahen hakula da illolin annobar corona suka tilasta wa dimbin mutane ficewa daga matsugunansu na asali . Shugaban kungiyar Voix Des sans Voix, Nassirou Saidou, na cewa dole ne hukumomi su yi takatsantsan da wasu bayanan da ke yawo a irin wannan lokaci .

Hauhawar farashin kayan abinci a kasuwannin kasashe irinsu Mali, Nijer, Najeriya, da Burkina Faso sanadiyyar matsalolin da ake dangantawa da yanayin da duniya ke ciki a yau, wani abu ne da ya taimaka wajen fadawar jama’ar yankin Afurka Ta Yamma cikin yanayin kuncin rayuwa a cewar rahoton na Oxfam.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG