A jamhuriyar Nijer, a yayin da direbobin motocin fisinja da na dakon kaya ke kokawa kan karancin man diesel a gidajen mai, kamfanin dillancin man fetur wato Sonodep na alakanta al’amarin da matsalar man da aka shiga a wasu kasashe makwabta sakamakon yakin Russia da Ukraine.
A Jamhuriyar Nijar an gudanar da bikin damkawa hukumomin kasar wata cibiyar da Majalisar Dinkin Duniya ta gina da hadin gwiwar wasu manyan kasashen duniya cikinsu har da Amurka domin karbar mutanen da suka tuba daga aika-aikar kungiyoyin ta’addancin da suka addabi jama’a a jihar Tilabery.
Bayan da ya je kasar Senegal, Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya isa birnin Yamai na Nijer inda ya gana da shugaba Mohamed Bazoum da mukarraban gwamnatinsa kafin ya ziyarci sojojin Jamus da ke aiyukan bada horo a karkashin rundunar hadin guiwar nahiyar Turai da ake kira La Gazelle.
A jamhuriyar Nijer wata kungiya mai zaman kanta ta kaddamar da ayyukan rajistar yara masu tawayar kwakwalwa da nufin tantance yawan irin wadanan bayun Allah dake bukatar a basu damar shiga makarantu tun suna kanana ta yadda watan-wata-rana zasu amfani kansu su kuma amfani al’umma.
Sai dai kawo yanzu, mutum daya tak ne aka gano a raye daga cikin wadannan dakaru.
A ranar 27 ga watan Nuwambar bara ne matasa suka datse mashigar garin Tera a wani lokacin da ayarin motocin sojan Barkhane ke shirin ratsa garin akan hanyarsu ta zuwa garin Gao, lamarin da ya sa Faransawan bude wuta akan wadanan mutane.
Laifukan da ake tuhumar sojojin sun hada da zargin yin fyade, batar kayan aiki sata da kuma arcewa daga aikin na soja.
A jamhuriyar Nijer masana sha’anin tsaro sun bayyana cewa matakin janyewa daga harkokin kungiyar G5 Sahel da gwamnatin mulkin sojan Mali ta dauka ba zai haifar wa kasar da mai ido ba, ganin irin muhimmiyar rawar da rundunar hadin gwiwar G5 Sahel ke takawa wajen yaki da ta’addanci a yankin Sahel.
Bayanai sun yi nuni da cewa wasu mata kan taimaka wa ‘yan ta’adda wajen shirya aika-aikar da suke tafkawa.
A washegarin darewarsa kujerar mulki shugaban kasar Nijar Mohamed Bazoum ya bukaci kungiyoyin fararen hula su ba shi goyon baya a yaki da cin hanci da mahandama dukiyar kasa
A cigaba da daukar matakan kare muhalli da duniya ke yi, an yi wani babban taro a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast, wanda wannan karon ya fi maida hankali kan yadda za a yaki kwararowar hamada musamman ma a yankunan Sahel da kewaye.
A jamhuriyar Nijer kungiyoyin mata musulmai sun gudanar da taron gangami domin tunatarwa akan hakkokin mata a Musulunci da kuma hanyoyin shawo kan matsalar yawaitar mutuwar aure, inda alkaluma ke nuna an samu mutuwar aure sama da 3,000 a shekarar da ta gabata a birnin Yamai kawai.
A jamhuriyar Nijer kungiyoyin manoma da makiyaya sun kaddamar da wata gidauniya da nufin tattara kudaden sayen babban hannun jari a bankin bunkasa ayyukan noma, wato BAGRI, bayan da aka fara yayata labarin yiwuwar bankin mallakar gwamnatin kasar zai koma hannun wasu ‘yan kasuwar waje.
Alkaluman mahukunta sun yi nuni da cewa makarantu sama da 800 ne matsalar tsaro ta yi sanadin rufe su a jihar Tilabery
Sai dai mambobin bangaren 'yan adawa a kasar irinsu Tahirou Guimba, na ganin alamun an yi zaben tumun dare.
Domin Kari