Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Ba Mahaman Ousman Rashin Gaskiya Kan Korafin Da Ya Yi A Zaben 2021


Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar
Mahamane Ousmane: Tsohon Shugaban Kasar Nijar

Kotun ta ce girman laifin da Ousman ke zargin an yi masa bai kai matsayin da za a biya diyya ba, ko kuma wani abin da ke kama da haka saboda haka ta bai wa bangaren hukumomin Nijar gaskiya. 

Kotun ECOWAS ta bai wa dan takarar jam’iyun adawa Alhaji Mahaman Ousman rashin gaskiya dangane da korafin da ya gabatar a bisa zargin mahukuntan Nijer da take masa hakkoki a yayin fafatawar da ta hada shi da dan takarar jam’iyar PNDS mai mulki Moahmed Bazoum a zaben 21 ga watan fabrerun 2021.

A zaman da ta yi a wannan Talata 31 ga watan mayun 2022 ne kotun ta CEDEAO mai ofishi a Abuja ta bayyana hukuncin da ta yanke a shari’ar da aka shafe watanni ana tafkawa bayan da tsohon shugaban Nijar bugu da kari dan takarar jam’iyun kawancen adawa Mahaman Ousman ya shigar da kara a bisa zargin cewa an tauye masa hakkoki a yayin zaben da aka ayyana dan takarar PNDS Tarayya Mohamed Bazoum a matsayin wanda ya yi nasara.

Kotun ta ce girman laifin da Ousman ke zargin an yi masa bai kai matsayin da za a biya diyya ba, ko kuma wani abinda ke kama da haka saboda haka ta bai wa bangaren hukumomin Nijer gaskiya.

Jigo a kwamitin zartarwar PNDS Tarayya shugaban matasa jam’iyar na kasa Daoui Ahmed Baringaye yace da ma sun san za a rina. Sai dai Kane Kadaure na cewa kada mage ba yanka ba.

A ra’ayin Daoui Ahmed bayan hukuncin na kotun ECOWAS ya kamata ‘yan kasar Nijar su gane cewa lokacin ce-ce-ku-cen siyasa ya kau.

Da kashi 55.66 daga cikin 100 na kuri’un da aka kada ne Mohamed Bazoum ya lashe zaben na 21 ga watan fabreru yayinda Mahaman Ousman ya sami kashi 44.34 daga cikin 100 a cewar hukumar zabe kafin daga bisani kotun tsarin mulki ta jaddada nasarar ta dan takarar jam’iyar mai mulki mafari kenan ‘yan hamayya suka garzaya kotun CEDEAO.

Saurari bayani cikin sauti daga soule Moumouni Barma:

ECOWAS Ta Ba Mahaman Ousman Rashin Gaskiya Kan Korafin Da Ya Yi A Zaben 2021- 2'56"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG