Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Fara Yunkurin Maye Guraben Ma'aikata 'Yan China Da 'Yan Kasarta A Matatar Man SORAZ 


Bazoum 
Bazoum 

Hukumoin Jamhuriyar Nijar sun bukaci shugabanin matatar man SORAZ su gaggauta yin bitar adadin ma’aikata ‘yan Nijer da ‘yan kasashen waje a ci gaba da shirye shiryen mayarda al’amuran gudanarwar matatar a hannun jami’ai ‘yan Nijer.

NIAMEY, NIGER - Wannan na faruwa ne kwana 1 kacal bayan da ministan man fetur ya umurci shugaban kamfanin CNPC na China ya kori wasu darektoci 2 ‘yan China da ake zargi da hannu a karancin man Diesel din da ake fama da shi a kasar.

A yarjejeniyar da bangarori suka cimma a yayin kaddamar da aiyukan matatar man SORAZ

Lura da yadda ake fuskantar jan kafa wajen soma zartar da matakan share fagen mayarda al’amuran gudanar da matatar man SORAZ a hannun ma’aikata ‘yan Nijar kamar yadda yake a yarjejeniyar dake tsakanin gwmamnatin ta Nijar da kamfanin CNPC na kasar China ya sa ministan man fetur Maman Sani Mahamadou ya umurci shugabanin matatar man su yi masa bitar adadin ma’aikata tare da fayyace matsayi da albashi da ainahin kasarsa.

Tuni aka fara yabawa da wannan mataki dake bukatar samun hadin kan daukacin ‘yan kasa. A cewar Shugaban kungiyar Voix des Voix Alhaji Nassirou Saidou ya zama wajibi shugaban kasa ya shiga gaban wannan sabuwar tafiya ta kare mutuncin kasa a idon abokan hulda.

A jajibirin daukan wannan mataki ministan na man fetur ya dibarwa shugaban kamfanin CNPC awoyi 48 domin ya kori wasu darektoci ‘yan kasar China 2 da ake zargi da hannu wajen kitsa wuyar gazoil wato man diesel dagangan a matatar SORAZ lamarin da wani jigo a kungiyar ROTAB, mai fafitikar ganin an yi adalci a sha’anin ma’adanai Mahamadou Tchiroma Aissami ke kwatantawa a matsayin wani sabon sauyi.

Amma wani mamba a kungiyar Sauvons Le Niger Salissou Amadou na ganin bukatar gudanar da binciken kokof don tantance zahirin abubuwan da suka wakana a tsawon shekaru sama da 10 da Nijer ta soma sayar da man fetur dinta.

A ci gaba da tsaftace wannan fanni ofishin ministan man fetur da na ministan kasuwanci sun yi kashedi ga dukkan masu gidajen mai su guji kara kudin mai don radin kansu matakin da tuni ya yi sanadin rufe wasu gidajen mai bayan da aka same su da bijirewa wannan umurni inji wata majiya

Saurari rahoto cikin sauti rahoto daga Soule Moumini Barma:

Nijer Ta Fara Yunkurin Maye Guraben Ma'aikata 'Yan China Da 'Yan Kasarta A Matatar Man SORAZ
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG