NIAMEY, NIGER - Tsohon shugaban Nijar Issouhou Mahamadou ne kungiyar ta dora wa nauyin shiga tsakani a kasar Burkina Faso, abinda ya haifar da mahawara a tsakanin ‘yan Nijar, yayin da wasu ke ganin zai samu nasarar sasanta bangarorin wasu kuwa cewa suke babu tabbas akan wannan hasashe, bisa la’akari da wasu dalilai.
Manzo na musamman na sakataren Majalisar Dinkin Duniya a Afrika ta yamma da yankin Sahel Mohamed Ibn Chambas ne kungiyar ta ECOWAS ta zaba domin shiga tsakani a rikicin kasar Guinea Conakry, yayin da shugaban Kasar Togo Faure N’yassimbe zai hada gwiwa da tsohon shugaban Najeriya Good Luck Jonathan don sasanta rigingimun kasar Mali, sai tsohon shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou da kungiyar ta dora wa nauyin warware rikicin kasar Burkina Faso, matakin da ke daukar hankulin jama’a a Nijar.
Mai sharhi akan al’amuran yau da kullum Abdourahamane Alkassoum na da kwarin gwiwar cewa Issouhou Mahamadou na iya samun nasarori a wannan aiki, koda yake akwai bukatar gyara a kudirin na kungiyar ECOWAS.
To amma a ra’ayin wani dan rajin kare dimokradiyya jagoran gamayyar kungiyoyin ROADD, Dambaji Son Allah zai yi wuya kwalliya ta biya kudin sabulu.
Rigingimun da suka yi sanadin faduwar daddadiyar gwamnatin Blaise Compaore da hatsaniyar siyasar da aka yi fama da ita a zamanin shugaba Kabore kafin daga bisani sojoji su tumbuke shi daga mulki alamomi ne da suka zama wajibi Issouhou Mahamadou ya yi la’akari da su don gane ta inda zai bullo wa aikin da aka ba shi.
Rashin daukar mataki a taron na CEDEAO na karshen makon da ya gabata game da takunkumin da aka kakabawa kasashen Mali, Guinea Conakry da Burkina Faso wani al’amari ne da a yanzu ke ci gaba da haddasa ce-ce-kuce a tsakanin jama’a domin abin na nuna alamun gazawar kungiyar.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: