Sama da mako guda kenan da man diesel ko kuma gas oil ya fara wuya a gidajen man Nijar musamman a garuruwan da ke kan iyakar kasar da Najeriya har ma da iyakarta da jamhuriyar Benin.
Lamarin da tuni ya fara shafar harkokin jigila kamar yadda wani jigo a hadakar kungiyoyin motocin suhuri ta UTAN Gamatche Mahamadou yayi korafi a kai.
A yanzu haka motocin daukar mai sama da 1000 ne ke can matatar man Soraz inda suka shafe kwanaki da dama suna jiran lodi sai dai babu alamar samun lodin a nan kusa-kusa, sanadiyar wannan matsala inji Mohamed Haiballa na kungiyar Drebobin motocin dakon man fetur.
Shugabannin kamfanin dillancin man fetur na Sonidep mallakar gwamnatin Nijar sun tabbatar da cewa ana fuskantar karancin man Diesel a kasar sakamakon yadda wasu suka fara ketarawa Najeriya da jamhuriyar Benin da man da ainihi aka yi tanadi domin bukatun cikin gidan Nijar.
Jamhuriyar Nijar wace ta fara sayar da man fetur din ta a shekarar 2011 na hako ganga 20000 a kowace rana wadanda ake tace su a matatar Soraz dake Damagaram, daga cikinsu akan ware ganga 7000 domin bukatun cikin gida yayinda akan sayar da ragowar ganguna ga kasashe makwafta.
To sai dai matsalar man da duniya ta shiga a sanadiyar mamayar da Russia ta yiwa Ukraine ta sa wasu masu harakar mai a kasashe makwafta suka fara ketarowa Nijar don saye abinda aka yi tanadi domin amfanin cikin gida yayinda hannun wasu ‘yan kasar ta Nijar ya tashi sakamakon wannan al’amari.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barma: