Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson, da kuma ministan tsaron gida John kelly, yau Alhamis ake sa ran zasu gana da shugaban Mexico Enrique Pena Nieto da ministocinsa, a mataki da ake jin shine na farko a jerin ganawa tsakanin manyan jami'an kasashen biyu da zai fi maida hankali kan safarar miyagun kwayoyi, da cinikayya da kuma batun shige da fice.
"Yana da muhimmanci ganin shugaban na Amurka ya aike da ministoci biyu zuwa Mexico a farko farkon kama aiki, inji kakakin fadar white House Sean Spicer jiya Laraba. "Wannan ya nuna alamujn irin kyakkyawar dangantaka da kasashen namu biyu suke da shi.
Jiya Laraban, kamfanin dillancin larabai nas Reuters, ya amabci ministan harkokin wajen Mexico Luis Videgray yana cewa "Mexico ba zata amince d a shirin shige da fice na kashin kai, kuma ba zata yi wata wata ba, wajen kai bartun gaban MDD ba.
Facebook Forum