Kasancewar akasarin kananan hukumomin jihar Neja na fama da matsalolin karancin kayayyakin more rayuwa, hakan yasa gwamnan ya fara wannan rangadi. A lokacin da tawagar gwamnan ta isa fadar mai martaba sarkin Kagara, Alhaji Salihu Tanko, gwamna yace ya fara wannan ziyara ne domin kanewa idanuwansa abin da ke faruwa a fadin jihar.
A cewar gwamnan daga fara wannan ziyara ya zantawa da wasu talakawan jihar a garin Wushishi, inda har ya bayar da umarnin a fara aiki cikin gaggawa kan matalolin da aka shaida masa.
Wasu mata dake garin Kagara, sun nemi taimakon gwamnan da ya samar da shirin da zai koyawa mata sana’o’i ganin yadda wahalhalun rayuwa ya kan wasu mata a wannan zamani.
Shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi jihar Neja, Gambo Tanko, yace akwai bukatar gwamnan ya sake kai musu tallafin kudaden wasu kananan hukumomi za su sami sukunin biyan albashi da kuma gudanar da wasu ayyukan ci gaban jama’a.
Duk da yake dai gwamna Abubakar Sani Bello, yace rangadin da yake na duba matsalolin jama’ar jihar ne, amma masu nazarin al’amura na ganin rangadin na da nasaba da yakin neman zaben tazarce a shekara ta 2019.
Domin karin bayani ga rahotan Mustapha Nasiru Batsari daga Minna.
Facebook Forum