Jami’an kasar ta Libya su kace bisa dukkan alamu an kule mutanen ciki ne har na tsawon kwanaki a kokarin tsallakawa dasu teku.
Wadanda wannan lamarin ya rutsa dasu ko ciki har da yarinya ‘yar shekaru 13 da wani yaro dan shekaru 14.
Haka kuma an samu damar kubutar da wasu mutane 56 a cikin wata kwantenar, sai dai wasu daga cikin su suna fama da mummunar rauni, wasu ma harda karaya.
Ma’aikatan jin kai ta ce yawancin mutanen daga kasar Mali suka fito.
Libya dai ta jima da zamowa kofar bullewar ‘yan gudun hijira dake kokarin tsallake tekun madataraniya domin zuwa Turai.
Rahotanni sun tabbatar cewa ‘yan gudun hijira da yawan su yakai 181,000 suka isa kasar Italiya ta wannan yanyar a cikin shekarar data gabata.
Ko a ranar laraban data gabata sai da aka ceto kusan yan gudun hijira da yawan su yakai 750, a gabar tekun kasar ta Libya, a wani aikin ceto da jami’an dake aiki gabar tekun Italiya suka yi wadanda kuma yawancin wadanda aka ceton yan Africa ne.
Facebook Forum