Hukumomin jinkai na Majalisar Dinkin Duniya (MDD) sun bukaci kungiyoyin taimako na kasa da kasa, dasu taimaka da kudi domin gudanar da ayyukan ceton rayukan jama’a a sassan da matsalar fari ta rutsa dasu a kasashen Habasha da Somalia, inda yanzu haka dubban mutane ke fuskantar barazanar mutuwa sakamakon yunwa.
A martanin Majalisar Dinkin Duniya (MDD) game da karancin abincin dake damun kasar Sudan ta Kudu, tace lamarin sai kara Kamari yake yi, hakan ya biyo bayan matsalar rashin zaman lafiya ne da kasar ke fama da shi tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen kasar.
Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Nikki Haley, ta fada jiya Talata cewa Amurka zata yi aiki da sauran kasashen Turai, duk da rashin fahintar da ake samu nan da can lokaci-lokaci a tsakanin juna.
Yayin da ‘yan Najeriya ke ta fadin albarkacinsu game da lafiyar shugaba Mohammadu Buhari, wanda yanzu haka ke London ana kulawa da lafiyarsa, gwamnan jihar Katsina ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yiwa shugaban addu’a.
A jiya ne alkalai a babbar kotu a nan Amurka suka yi raba dai-dai a ra’ayin su, akan ko iyayen nan ‘yan kasar Mexico na iya shigar da kara a kotun Amurka game da wani wakilin Amurkan da ya harbe dansu a kan iyakar kasar Amurkar da Mexico.
Wasu ‘yan bindiga sun jefa wani yanki na babban birnin tarayyar Najeriya cikin duhu, biyo bayan awon gaba da su kayi da wayoyin samar da hasken wutar lantarki.
Ma’aikatar harkokin Mata ta Tarayya da takwararta ta jihar Borno sun fara horas da wasu mata da suka tsinci kansu cikin mawuyacin hali sana’o’i daban-daban.
Yayin da rikicin Boko Haram ya fara lafawa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, jihohin da lamarin ya shafa na kokarin farfadowa ta hanyar samarwa matasa ayyukan yi.
Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da sabon Mai Ba Da Kasa Shawara Kan Tsaro, Laftana-Janar H.R. McMaster, wani kwararre kan dabarun matakan soji wanda ya dade ya na aikin soji.
Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence jiya Litini ya jaddada matukar goyon bayan da Amurka za ta ci gaba da nuna ma NATO da Turai.
Dubban masu zanga-zanga sun yi gangami a fadin kasar Amurka na bayyana rashin amincewarsu da gwamnatin Donald Trump a jiya Litini, wadda ita ce zagayowar Ranar Tunawa da Shugaban Amurka na farko.
Dadadden Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, Vitaly Churkin, ya mutu ba zato ba tsammani jiya Litini a birnin New York, kwana guda kafin ya cika shekaru 65 da haihuwa.
Sakataren Tsaron Amurka Jim Mattis ya fadi jiya Litini cewa, Amurka ba ta da niyyar kwace man kasar Iraki, wani abin da a baya shugaba Trump ya ba da shawarar a yi, a matsayin ganimar yakin da sojojin Amurka ke yi a can, kuma saboda a hana kungiyar ISIS samu ta sayar.
Jami’an tsaro sun yi yunkurin dakatar da wani taron jam’iyyar PDP bangaren Sanata Ahmed Makarfi a Abuja, yayin da bangaren Makarfin ke zargin gwamnatin APC da hada baki da bangaren Sanata Ali Modu Sheriff, don wargaza jam’iyyar PDP.
Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 21 ga watan Fabarairu a matsayin ranar inganta harshen uwa a Duniya.
Tsohon Manajan Daraktan kamfanin Mai na Najeriya NNPC, Mr Andrew Yakubu, ya bukaci babbar kotun tarayya dake Kano ta soke odar da ta bayar kan mallakawa gwamnatin taraiya Dala Miliyan 9 da dubu dari 8 da hukumar EFCC ke zargin ya sace.
Noma Tushen Arziki
A Somalia, jami'an kasar suka ce akalla mutane 30 ne suka halaka wsu da dama kuma suka jikkata lokacin da wani gagarumin bam da aka boye cikin wata mota ya tashi cikin wata kasuwa yayin da take cike da mutane a Mogadishu jiya Lahadi.
Mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, a karon farko tun bayan da ya kama aiki, yana ziyara a Turai.
Shugaban Amurka Donald Trump, zai fito da sabuwar dokar da zata hana baki daga wasu kasashen 7 da galibin al'umarsu musulmi ne zuwa Amurka, sai dai wannan karon sabuwar dokar "za'a ingantata" kuma za'a aiwatar da ita ba tare da rudani da aka fuskanta tattare da dokar ta farko. Kamar yadda ministan tsaron cikin gidan Amurka John kelly yayi bayani.
Domin Kari