Wolfsthal, yace a wata ganawa tsakanin tsohon shugaban na Amurka da Mr.Trump, ya gayawa masa cewa tilas sabon shugaban ya tunkari barazanar Nukiliya da makamai masu linzami daga Koriya ta Arewa.
Kamar yadda Mr. Wolfsthal yayi bayani, gwamnatin Obama ta gabatarwa Trump zabi biyu wajen tunkarar barazana daga koriya ta arewa, na daya ta wajen gudanar da shawarwari da kasar kai tsaye,ko kuma a kara matsin lamba kan koriya ta arewa ta matsawa uban dakinta China lamba.
Muriyar Amurka ta nemi majalisar tsaron kasa ta bata takaitaccen bayani kan manufofin sabuwar gwamnatin kan koriya ta arewa, amma har yanzu bata sami amsa ba.
Mr. Wolfsthal dai ya rike mukamin hadimi kuma babban darekta kan kayyade hayayyarfar makaman kare dangi a majalisar tsaron kasa.
Facebook Forum