A jiya Talata, Ministan harkokin cikin gida na Faransa Gerard Collomb, ya ce mutumin da ya kaiwa ‘dan Sanda hari da guduma a harabar cocin Notre Dame a Paris, yayi ihun cewa “hakan ramuwa ce ga Syria.”
Biyo bayan jerin hare-haren ta’addanci da aka kai cikin wannan makon, Birtaniya zata gudanar da babban zabenta ranar Alhamis, kuma batun matakan tsaro ya zamanto kan gaba.
Fadar shugaban kasar Amurka ta White House ta ce shugaba Donald Trump da sarkin Saudiyya Salman bin Abdul’ziz, sun tattauna ta wayar talho, kuma suka jaddada bukatar da ke akwai ta hadin kan kasashen yankin Gulf biyo bayan shawarar da kasashen larabawa suka yanke na katse hulda da kasar Qatar
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta yi gargadin cewa Amurka zata fice daga cikin hukumar kula da 'yancin Bil Adama ta Majalisar idan har hukumar bata yi wasu sauye-sauye ba.
Wani alkalin kutun Tarayya a Legas Justice Muslim Hassan, ya mallakawa gwamnatin tarayya makudan kudaden da hukumar EFCC ta kama a wani gida dake unguwar Ikoyi a kwanakin baya.
Yayin da ‘yan Najeriya musamman maniyyata aikin hajjin bana ke ci korafi da game farashin kujerar aikin hajji da hukumar alhazan kasar ta kayyade, na fiye da naira miliyan guda da rabi ga kowane Alhaji.
Noma Tushen Arziki
Daruruwan ‘yan gudun hijira na cikin gida a arewacin kasar Kamaru, suna kauracewa sansanan dake kusa da kan iyaka da Najeriya, bisa ga cewarsu, yanzu rayuwarsu na cikin hadari, biyo bayan hare haren kunar bakin wake da aka kai, yayinda gwamnati ke kira da a kwantar da hankali.
Batun yunkurin dawo da shingayen biyan kudaden a kofar shiga manyan biranen Najeriya da kuma karin farashin man fetur daga 145 zuwa 150 na neman tayar da hankalin ‘yan Najeriya, musamman direbobin motocin haya dake jigilar fasinjojin tsakanin sassan kasar.
Babban hafsan sojan mayakan ‘kasa na Najeriya Janar Tukur Buratai ya ce cikin watannin Satumba zuwa Oktoba masu zuwa ake sa ran bude sabuwar Jami’a mallamar sojojin Najeriya a garin Biu dake kudancin Borno.
Kimanin mutane shida ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan sama da ta mamaye wasu garuruwa guda takwas a kananan hukumomi uku dake jihar Neja a Najeriya.
A wata sabuwa kuma shugaban Amurka Donald Trump yace ya kamata duniya ta daina siyasa a yaki da ta’addanci, ya kuma yi nuni da mummunan harin da aka kai birnin London ya sabonta kiransa ga kotuna da su tabbatar da umarninsa na hana kasashe shida masu yawan Musulmi shigowa Amurka.
Babbar jami’iyar adawa a Cambodia ta taka rawar gani a zaben kananan hulumomi a jiya Lahadi wanda ke yin barazana ga Firayi Minista Hun Sen dake rike da mulki.
Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai mummunar harin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da yammacin shekaranjiya Asabar a birnin London, inda mutane bakwai suka mutu wasu 48 kuma suka jikata.
Masana da kwararru kan aikin jarida a Amurka da na kasashe masu tasowa irin su Najeriya na ci gaba da yin tsokaci dangane da irin rawar da kafafen labarai na kasashen yamma ke takawa na bada rahotannin da suka shafi Afirka.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, ya daina jagorantar tattaunawar kasa da ake gudanarwa. Mataimakin shugaban dandalin Angelo Beda ya fada jiya alhamis cewa, shugaban kasar ya ajiye mukaminsa na uba, yanzu tsarin yana hannun al’ummar kasar Sudan ta Kudu.
Amurka ta kafawa wadansu kamfanoni tara, da kuma wasu mutane uku takunkumi, wadanda aka hakikanta suna da alaka da ayyukan makamai masu linzami na Koriya ta Arewa, bisa ga cewar ma’aikatar kudin Amurka.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, Amurka zata janye daga yarjejeniyar da aka cimma a birnin Paris da ta shafi canjin yanayi.
Albarkacin watan Ramadan gidauniyar Indimi Foundation dake jihar Borno, ta taimakawa ‘yan gudun hijira da gajiyayyu da tallafin kudade da kayayyakin abincin na miliyoyin Nairori.
Domin Kari