Yayin da wasu shugabannin Afirka ke korafin kafafen labaru na kasashen yamma na watsa labaran farfaganda akansu, amma masana irin su Farfesa Rosental Alves, babban malami a sashen koyon aikin jarida a jami'ar Texas dake Austin, ya ce shi baiga wata farfaganda da ake yadawa akan kasashe masu tasowa ba, hasali ma kafafen yada labaran na taimakawa wajen tsage gaskiya komi dacinta da hakan ke taimakawa wajen inganta al'amura.
Farfesa Alves, ya ce labarai da ake bayarwa da suka shafi cin hanci a kasashe masu tasowa na taimakawa kasashen da ma su kansu shugabannin.
Malami a sashen koyon aikin Jarida a jami'ar Ahmadu Bello Dr. Kabiru Danladi Lawanti, ya ce tsarin watsa labarai a kasashen yamma da na Afirka ya sha banban, galibin kafafen labaru na Afirka basa maida hankali kan hakikanin abin dake gudana yayin da su kuma na manyan kasahe ke tsage gaskiya komi dacinta.
Shima kwararren dan jarida Babayola muhammadu Toungo, cewa yayi galibin jama'a a kasashe masu tasowa basu da aminci ga kafafen watsa labaru na cikin gida.
Domin karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum