A ranar 11 ga watan Afrilun wannan shekarar ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, ta kama wasu makudan kudade a wani gida mai lamba 16 titin Osbon, dake unguwar Ikoyi.
Hukumar dai ta gabatar da kudaden gaban kuliya domin cigiyar wanda ya mallaki kudaden da ya je gaban kotu domin ya karba. Sai dai kuma har ya zuwa wannan lokaci da kotun ta yanke hukuncin, alkalin kotun ya bayyana cewa babu wani da wanda ya gabatar da kansa a matsayin wanda ya mallaki kudaden.
Da farko dai babban daraktan hukumar leken asirin kasashe, Mista Ayodele Oke, ya bayyana cewa kudaden na hukumar NIA ne, sai dai kuma bincike ya nuna cewa gidan da aka sami kudaden gida ne da wani mai kamfani da mai ‘dakinsa suka mallaka, lamarin da yasa aka dakatar da darakta Oke daga kan mukaminsa.
Haka shima gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bayyana cewa kudaden mallakar gwamnatin jihar Rivers ne da yayi zargin cewa tsohon gwamna Chibuike Amaechi, kuma ministan sufuri a Najeriya shine ya wawure a lokacin da ya ke kan karagar mulki. Sai kuma har lokacin yanke wannan hukunci babu wata shaida da aka gabatar dake nuna cewa kudaden mallakar gwamnatin jihar Rivers ne.
Wannan hukunci da kotun ta zartar yazo ne a dai-dai lokacin da kwamitin da ke ba shugaban ‘kasa shawara akan yaki da cin hanci da rashawa ya bayyana cewa kimanin mutane 55 ne da suka hada da jami’an gwamnati da kuma ‘yan kasuwa suka sace kwatankwacin Naira Tiriliyon ‘daya da rabi a zamanin tsoffin shugabannin Najeriya, irin su Obasanjo da marigayi ‘yar Aduwa da kuma Good Luck Jonathan.
Domin karin bayani ga rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum