Rahotanni sun nuna cewa yanzu haka akwai daruruwan mutane da suka rasa muhallansu tare da abinci sakamakon ambaliyar ruwan da ta shafi kananan hukumomin Mashegu da Bargu da kuma Agaye.
Shugaban karamar hukumar Mashegu, inda lamarin ya fi ta’azzara Alhaji Sa’idu Shu’aibu Kaboji, ya ce duk da yake har yanzu ba a kammala kididdigar ba, amma akwai kimanin mutane dubu shida wadanda basu da gidaje da abincin da zasu ci.
A can karamar hukumar Bargu kuwa, ambaliyar ta tafi da gidaje sama da 200, haka kuma anyi asarar dabbobi masu yawan gaske.
A halin da ake ciki dai yanzu, gwamnatin jihar Neja ta ce ta fara shirin kai ‘doki ga wadanda lamarin ya shafa, shugaban hukumar agajin gaggawa ta jihar Neja Alhaji Ibrahim Inga, ya ce yanzu haka suna kokarin samarwa da mutanen abinci da guraren kwana na wucin gadi.
Jihar Neja na daya daga cikin jihohi biyar da rahotan masu hasashen yanayi ya nuna cewa za a samu ambaliyar ruwan.
Domin karin bayani ga rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum