Sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fara jan ragamarsa da soke tallafin man fetur, baya ga wasu jerin alkawura da ya yi.
Shin wadanda su ka lashe zabe za su cika alkawarin kyautata rayuwar matasa ko sun yi zane kan ruwa ne, matasan sun duba matakan dogaro da kai maimakon jiran gawon shanu.
An tsaurara matakan tsaro a Abuja gabanin rantsar da Bola Tinubu a matsayin sabon shugaban kasa ranar Litinin mai zuwa.
Wanda ya fara kwarmato a Najeriya Dr. George Uboh ya ce shirin kwarmaton da kuma asusun bai daya na tarayya na daga shirye-shiryen gwamnatin Buhari da a ka samu tangardar aiwatar da su.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai koma Daura ya kula da shanunsa bayan ya kammala wa'adinsa karo na biyu.
Wasu 'yan kungiyar gani-kashenin zabebben shugaban Najeriya Bola Tinubu su ce sun cika kwanaki 56 su na kange dandalin UNITY daga magoya bayan dan takarar jam'iyyar Leba Peter Obi.
Zaben dai ya samu fafatawa da matasa inda a ka samu wasu daga cikin su ma sun lashe zabe musamman a majalisun dokoki.
Sanarwar ma'aikatar wajen ta kara da cewa tawagar tana dauke ne da mutum tara 'yan Najeriya inda biyar daga cikin su ma'aikatan ofishin jakadancin Amurka ne a Najeriya yayin da biyar daga ciki jami'an 'yan sandan kasar ne.
Masu ruwa da tsaki da wasu ‘yan Najeriya a kusan kowane bangare na bayyana mabambantan ra’ayoyi kan mulkin Shugaba Muhammadu Buhari, a yayin da a ke kimanin mako biyu shugaban ya yi ban kwana da fadar gwamnatin kasar.
Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin ta Najeriya NBC ta sha alwashin daukaka kara kan hukuncin babbar kotun tarayya da ya haramta ma ta cin tarar kafafen yada labaru da su ka saba doka.
Sabbin 'yan majalisar wakilan Najeriya sun ce za su hada kai don magance zargin da a ke yi wa majalisa na zama 'yar amshin shatan sashen zartarwa.
Hankalin 'yan Najeriya ya koma kan sauran dalibai da su ka makale a kan iyakar Sudan da Masar bayan isowar rukunin farko na 'yan Najeriya 366 sun iso gida.
Wannan kira na daga manyan bukatun da kungiyar ta gabatar a bikin ranar ma'aikata ta bana.
INEC na mayar da martani ne kan wasikar da Hudun ya rubutawa babban sufeton kan dalilansa na ayyana sakamakon zaben na jihar Adamawa.
Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya ta bayyana cewa gwamnati na daukar matakan dawo da ‘yan Najeriya gida don kauce wa rikicin Sudan ta hanyar kasar Masar.
Domin Kari