A karshen makon nan ne za a rufe hanyoyin tsakiyar birnin tarayya Abuja da su ka nufi hanyar filin Eagle Square, inda za a yi taron rantsar da sabuwar gwamnati ta Bola Ahmed Tinubu.
Kama daga sojoji zuwa 'yan majalisar zartarwa sun yi tarukan bankwana da shugaba Muhammadu Buhari wanda zai bar Abuja zuwa Daura kai tsaye daga filin Eagle Square, wanda haka ne al'adar tun 2007 da Obasanjo ya tafi Abeokuta a jihar Ogun, Jonathan kuma ya tafi Otuoke a jihar Bayelsa a 2015.
Tuni dai aka yi addu'o'i a masallacin Abuja, a ranar Lahadi kuma za a yi addu'ar zaman lafiya a babbar majami'ar tarayya.
Muktari TBO, na daga cikin magoya bayan Buhari tun shigar sa siyasa, ya ce ba abin da za su ce da ya wuce mulki ya kammala lafiya.
Shi kuma Injiniya Zakari Nguroje, wanda ke cikin wadanda za su halarci bikin rantsarwar na fatan Tinubu zai tuna da yankin arewacin kasar.
Shugaba Buhari ya bukaci wadanda ba su ji dadin matakansa ba su yafe masa. Shugaban dai ya sha neman talakawa su dage wajen mara ma sa baya.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: