Hukumar NBC wacce ke ba da lasisi ga dukkan kafafen rediyo da talabijin a Najeriya, kan soke lasisi ko cin tarar duk kafar da ta keta jerarrun ka’idoji a yayin yada shirye-shirye.
Alkalin babbar kotun taraiya James Omotosho, ya yanke hukunci kan karar da wata kungiya mai da'awar kare muradun kafafen labaru ta shigar don dakatar da NBC daga cin tarar kafafen, tare da nuna cewa hukumar ba ta hurumin yin hakan don ita ba kotu ba ce.
Alkali Omotosho, ya soke tarar da NBC ta ci kafafe 45 Naira dubu 500 a shekarar ta 2019, wacce ta haddasa shigar da karar a bara.
Hakan na nuna matukar hukumar NBC na da korafi kan wata kafa sai dai ta shigar da kara kotu, inda shari'a za ta yi halin ta.
Shugaban hukumar NBC Balarabe Shehu Illela, ya ce za su nazarci hukuncin da zummar daukaka kara don sam ba su gamsu da matsayar alkalin ba.
Da ya ke duba lamarin bisa dokokin Najeriya Barista Mainasara Kogo Umar, ya ce ba mamaki lauyoyi ba su yi tsayin daka wajen kare hurumin hukumar ba ne, don ba zai yiwu a kyale kafafe su rika cin karen su ba babbaka ba.
Shugaban na NBC bai yi wani zargi kan mai shari'a Omotosho kan hukuncin ba, don ya yi aiki ne bisa kujerar sa ta alkali.
Hukumar NBC na yin wani shiri na yi wa hatta kafafen labarun ketare da ke ma'aikata a Najeriya rejista, don ja mu su birki a labarun da ke cin karo da muradun gwamnatin kasar, amma hakan ya samu suka don tunanin hanyar dakile fito da labarun gaskiya ne ba kwane-kwane.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya: