Masanin kimiyyar siyasar duniya na jami’ar Bayero ta Kano Dr. Sa’idu Ahmed Dukawa ya ce kasashen Afurka da dama za su yi juyayin mutuwar sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu don rawar da ta taka wajen karbar ‘yancin su.
Shirin wannan makon ya tabo batun illar yada jita-jita ko farfagandar karya ta hanyar daukar hirar wasu kamar ta zancen wayar tarho don isar da wasu sakonni da za a yi tsammani na sirri ne alhali duk shiri ne na muzanta wasu abokan hamayya.
Masana kimiyyar siyasa na bayyana cewa kalubalen tattalin arziki da matsalolin da ta gada daga gwamnatin Boris Johnson, su ne mafi girma dake gaban sabuwar Firai Ministar Burtaniya Liz Truss.
Matasa mazauna karamar hukumar Karu sun bayyana yadda dokar ta shafi rayuwarsu ta yau da kullum musamman masu kananan sana'o'in da su ke yi don samun kudin shiga.
Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci gwamnatin Najeriya ta fitar da matsaya kan wadanda a ke tuhuma da hannu a kisan gilla ga babban malamin nan na Islama a Yobe Sheikh Gwani Aisami.
Kwararre kan aiyukan ganowa da hako man fetur Dakta Mubarak Ibrahim Mahmud, ya ce idan Najeriya za ta iya tace man da ta ke bukata a cikin gida, da arziki ya wadaci kasar.
Kasuwar canjin kudi ta Abuja da a ka fi sani da ZONE 4 ta yanke matsayar rage farashin dala daga sama da Naira 700 a makon jiya zuwa Naira 630.
Ana ci gaba da samun baraka a manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya. Ta baya bayan nan da ta tsuduma cikin babbar rigima ita ce PDP wadda takaddamar Atiku da Wike ke girgiza ta.
Tabarbarewar tsaro a sassan Najeriya na kara firgita jama’a don yanda ba wanda ya tsira tsakanin fararen hula a kan titi da su kan su jami’an tsaron.
Majalisar dattawan Najeriya na son bayani daga gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele kan yadda Naira ke cigaba da faduwa a kusan duk mako kan canjin dalar Amurka.
Mataimakin Shugaban Najeriya Yemi Osibajo ya bayyana dalilinshi na kin fita kasar waje domin yin jinyar gurdewar da ya yi a kafa yayin motsa jiki.
Kungiyar gwamnonin APC ta mara baya ga zaban Kashim Shettima a matsayin mataimakin Bola Tinubu a takarar zaben 2023.
Dan takarar jam’iyyar APC a zaben Najeriya mai zuwa na 2023 Bola Ahmed Tinubu ya ce ya zabi tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima ya zama mataimakin sa a takarar don ya cancanta ne.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana barayin daji da sauran ‘yan ta’adda a matsayin masu izgilanci da za a yi maganin su, a lokacin da ya je Daura bikin babbar Salla.
Kisan gilla ga tsohon firaministan Japan Shinzo Abe ya zo wa masu sharhi da mamaki a kasar da ta ke daukar tsauraran matakai kan amfani ko mallakar bindiga.
Sha’irai ko mawakan yabo ga Manzon Allah su 5 da su ka lashe gasar baituka da a ka gudanar a Zaria, sun ce sun ji shiru wajen cika musu alkawarin kujerun Makkah daga dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu har a na jajiberin hawa arfa a hajjin bana.
Ga dukkkan alamu, shirin ziyarar Shugaba Buhari zuwa Daura na nan daram, duk kuwa da tauna tsakuwar da 'yan ta'adda su ka yi.
Domin Kari