Dakta Ibrahim wanda mawallafin littattafai ne na neman fetur da lamuran tashoshin jiragen ruwa, ya ce Najeriya na shan faman rasa arzikin ta da yawa don sayar da danyen mai da shigo da tatacce.
Masanin wanda ya yi aiki a tekun Gulf of Gunea, inda Najeriya ke tono mai a teku, ya lissafa arziki da yawa da a ke fitarwa daga jikin man fetur tamkar saniya da a kan amfana da naman ta, fatar ta, nonon ta, kahon ta da sauarn su.
Dakta Ibrahim ya alakanta matsalolin rashin aikin matatun fetur din da asalin tarihin yanda kasashe masu ci gaban masana’antu su ka zuba jari a hakar fetur, ta hanyar manyan kamfanonin ‘yan jari hujja da ba sa barin wani abu ya dakatar da ribar su.
A nan masanin ya ba da shawarar Najeriya ta yi kokarin kafa kananan matatun fetur a yankuna daban-daban, da ba su da tsadar gudanarwa inda hakan zai sa dukkan arzikin har da dusar man ya zama ya na amfanar yan kasa.
Masanin tattalin arziki a Abuja Yusha’u Aliyu, ya ce ko dai ba za a iya tabbatar da matatun man kasa ba, gwamnati za ta iya jawo kamfanonin ketaren su kafa matatun a Najeriya.
Yusha’u Aliyu ya kara da cewa arewa ta fi samun cikas don ba a gama batun tono mai a yankin ba balle a yi magana cin gajiyar matatun man.
Gwamnatin Najeriya ta sha baiyana muradin fadada hanyoyin tattalin arziki dan rage dogaro da man fetur, inda ya zama hatta a man fetur din ba a samun cin gajiyar kammalalliyar riba.
Sauraro rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya: