A karo na farko a tarihi, an kaddamar da kwafin fassarar Alkur’ani Mai Girma a harshen Igbo da Sheikh Murtala Chukwuemeka Ohajimadu ya fassara.
Alamu na nuna wasu jam’iyyu da a baya ba su da tagomashi na samun ‘yan takara takarar mukaman zaben 2023 mai zuwa.
Shirin har ila yau, ya duba tambayar shin fidda kudi kawai kan samar da tsaro ne maslaha ko sai an raka da sanya idanu da ba da hadin kai?
Mataimakin dan takarar jam’iyyar APC na shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu wato Ibrahim Kabir Masari ya ce ko rana daya tak aka ba shi dama ya rike matsayin takarar ya gamsu.
Wata tawaga ta kungiyar nakassassu ‘yan jam’iyyar APC ta gudanar da zanga-zanga a shalkwatar jam’iyyar don nuna rashin amincewa da zaben Tolu Bankole a matsayin shugaban nakasassu na jam’iyyar alhali sun ce ba shi da wata nakasa.
Lauya mai zaman kan sa a Abuja Barista Buhari Yusuf ya ce akwai tanadin hakan a sabuwar dokar zabe.
Jam’iyyar APC mai mulki ta mika sunan dan takararta na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin takarar sa Kabir Ibrahim Masari da a ka boye sunan sa.
A jam'iyyar APC mai mulki da lamarin ya fi daukar hankali, har yanzu ana kan tantance sunaye.
Karyar da a ka yada kwanaki kan wasu kalamai da aka ce daga tsohon sakataren gwamnati Babachir David Lawal ta kawo rudani kafin a gano gaskiyar lamarin.
Najeriya kasa ce da ke da al'umomi masu bin addinai mabanbanta da kuma kabilu daban-daban a sassanta.
An samu rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin jam’iyyar APC da hakan ya kawo tarnaki ga zaben fidda gwani dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.
Sahihan bayanai na nuna cewa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na daukar matakan karshe don cankar wanda su ke ganin ya dace ya zama dan takararsu a babban zaben 2023, wannan na zuwa ne bayan zabar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP.
Irin wannan hanya za ta bullo da hanyoyin samun kudi ba da dogaro kacokan ga kudin da jihohin kan samu a wata daga gwamnatin taraiya ba.
Jam’iyyar APC mai mulki a tarayyar Najeriya na shirin gudanar da zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa da ‘yan takara 23.
Tsohon sakataren gwamnatin Najeriya Babachir David Lawal ya ce sai 'yan arewa sun kaunaci juna ta hanyar kaucewa bambancin kabilanci za su samu dawo da tagomashin yankin kwatankwacin yanda ya ke a Jamhuriya ta farko.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe tikitin zaben shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP.
Shirin har ila yau ya tabo batun matsalar makiyaya da manoma a yankin karamar hukumar Jama'a da ke kudancin jihar Kaduna a Najeriya.
APC ta jaddada cewa za ta gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a inuwar jam'iyyar ranar lahadi 29 ga watan nan.
‘Yan takarar shugaban kasa na manyan jam’iyyu na cigaba da zaga jihohin da musamman su ke da yawan wakilai don neman goyon baya a zaben fidda gwani.
Masu sharhi sun ce bude tashosin zai samar da ayyukan yi ga matasa a yankin na arewacin Najeriya da ba shi da iyaka da teku.
Domin Kari