Bayan gasar da a ka gudanar a fadar Mai Martba Sarkin Zazzau a 2020, shugaban kungiyar tallafawa Tinubu TSO Aminu Sulaiman ya mika kofin ALKUR’ANI da kuma alkawarin ba da kujerun Makkah daga Tinubun.
Kasancewar dakatawar zuwa Makkah na tsawon shekaru biyu don kalubalen cutar annoba, ya sa sha’iran karkashin kungiyar Majama’u Rijalil Tijjaniyya, jira da kuma tsammanin samun kujerun bana tun da Najeriya ta samu Kason kujeru dubu 43.
Kakakin wadanda su ka lashe gasar Dogon Bege wanda shi ne ma Khalifan shahareren Sha’iri marigayi Rabi’u Usman Baba, ya nuna takardun godiya da Mai Martaba Sarkin zazzau Alhaji Ahmed Bamalli ya aikatawa Tinubu da shugaban magoya baya ya rantabawa hannu.
Dogon bege ya bukaci Tinubu ko mukarraban sa, su duba yin wata diyya ga wannan alkawari don kare martabar su a wajen sha’iran.
Duk kokarin jin ta bakin Aminu Sulaiman ya ci tura. Shi kuwa mataimakin takarar Tinubu, Ibrahim Masari, bai yi wata-wata ba wajen cewa Tinubu bai san da wannan labari ba amma dai in Allah ya kai rai badi zai duba batun kujerun.
Mawakan bege da kan rera waka a wajajen tarukan majalisi, maulidi da sauran su, na tara jama’a da magoya baya daga ‘yan darikar Tijjaniyya da Kadiriyya.
Mutum 5 da su ka lashe gasar sun hada da Malam Habibu Kebbi, Malam Aminu Sirrin Bege Kaduna, Malam Zilkifulu Dogon Bege Malumfashi, Malam Bashir Kano da Malam Hassan Maska.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: