Madugun kamfen din samun tikitin dan takarar APC Bola Tinubu, Babachir David Lawan ya fito karara ya ce bai ga yadda Tinubu zai lashe zaben 2023 ba tun da bai dauki kirista mataimaki ba.
Zaben sabbin shugabannin uwar kungiyar Fulani makiyaya ta “MIYETTI ALLAH” ya bar baya da kura don daya daga ‘yan takara ya ce bai amince da sakamakon zaben ba.
Samame a kasuwar canjin ya haddasa sanya wasu ‘yan kasuwar buya inda har ta kai ga EFCC ta kama wasu daga cikin ‘yan kasuwar amma daga bisani ta sake su.
Dama jihar na fuskantar kalubalen tsaro daga musamman masu satar mutane da a ka fi fama da su a sassan karamar hukumar Isah da Sabon Birni.
Matasan sun ba da shawara kan hanyoyin da za a bi wajen dawo da salama a jihar ta hanyar saita kwakwalwar matasa zuwa dabi’u nagari.
Yayin da aka yi bankwana da ambaliyar ruwa a wasu sassan duniya, har yanzu akwai fargabar wannan matsalar da dangoginta a sassan Najeriya
Gwamnan jihar Binuwai Samuel Otom ya yi amfani da damar ganawa da gwamna Bala Muhammad na Bauchi wajen ba da hakuri ga kalaman da ya furta cewa sam ba zai zabi Bafulatani a matsayin shugaba ba, da cewa, gara ma ya mutu da ya goyi bayan Bafulatani.
Matasan sun ba da shawarin hanyoyin da za a bi wajen dawo da salama a Jihar ta hanyar saita kwakwalwar matasa zuwa dabi’u nagari.
Hukumar zaben wacce ta kammala zagaye na karshe na sabunta rejistar gabanin babban zaben 2023, ta baiyana filla-filla irin matakan da ta kan bi gabanin yin rejistar.
Shugabar kwamitin zabe ta Majalisar Wakilan Najeriya Aisha Jibir Dukku ta jaddada cewa, an tsara zaben 2023 ta hanyar da a ka toshe duk wata kafa ta magudi.
Dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam’iyyar APC mai mulki, Bola Tinubu, zai kaddamar da kamfen a ranar 15 ga watan Disamba a Jihar Filato bayan tsawon lokaci tun bude kamfen da hukumar zabe ta yi a ranar 28 ga watan Satumba.
Wata majiya ta ce jami’an sun tafi da akalla mutum 80 wadanda a lokacin hada wannan rahoto ake kokarin belin su.
Kan lamuran tsaro, Kwankwaso ya ce zai kara yawan jami’an sojoji zuwa miliyan daya haka nan ‘yan sanda ma za su zama miliyan daya.
Darajar Naira na kara kasa a canjin dala inda hakan ke karfafa fargabar kara tashin farashin muhimman kayan masarufi.
Magoya bayan ‘yan takarar shugabancin Najeriya na nuna yanda gwanayensu su ka yi zarra kan juna, yayin da kamfen din zaben 2023 ya fara kankama.
An samu mafi munin ambaliyar ruwa a ‘yan shekarun nan a Najeriya musamman in an kwatanta yawan mutanen da su ka yi asarar rayukansu. Mutuwar mutum 603 a fadin Najeriya ya ninka yawan wadanda su ka rasa rai a bara a sanadiyyar ambaliyar.
Ofishin dan takarar jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya ce dan takarar na su ya ki zuwa zauren baje kolin manufofin ‘yan takara a gidan AREWA a Kaduna, don zargin taron na da manufar mara wa wani dan takara baya.
Mahmud Yakubu wanda ke magana a wata ziyara a Amurka a taron da asusun raya dimokradiyya da kuma asusun tallafawa tsarin zabe na duniya su ka shirya, ya ce labarun karya ya zama kalubale da ke kawo damuwa kan babban zaben Najeriya.
Domin Kari