Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda EFCC Ta Kai Samame Kasuwar ‘Yan Canji A Abuja


Ofishin EFCC a Abuja
Ofishin EFCC a Abuja

Wata majiya ta ce jami’an sun tafi da akalla mutum 80 wadanda a lokacin hada wannan rahoto ake kokarin belin su.

Jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, sun kai samame kasuwar ‘yan canji da ke unguwar Zone 4 a Abuja, babban birnin kasar.

Bayanai sun nuna cewa jami’an hukumar sun kai samamen ne sanadiyyar tsananin tashin farashin dala da ake fuskanta a Najeriya.

A yanzu haka dala daya ta haura naira 800 har ma ana hasashen ta kai naira 900.

Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El Hikaya, ya ruwaito cewa an ga jami’an sun girke motocinsu biyu a kan magamar hanya inda suka yi yunkurin tafiya da wasu masu canjin kudin.

Wata majiya ta ce jami’an sun tafi da akalla mutum 80 inda a halin yanzu a ke yunkurin neman belin su.

An fahimci cewa masu neman canja kudinsu daga naira zuwa dala ne su ka haddasa tashin farashin kudin don kaucewa zuwa banki da hakan zai sa a gano makudan kudin da suka adana.

A makon da ya gabata, babban bankin Najeriya ya sanar da shirin sauya fasalin wasu daga cikin kudaden kasar da suka hada da takardun Naira 200, 500 da kuma 1,000.

Cikin wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar wacce ta nuna goyon baya ga shirin sauya fasalin kudin, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce matakin zai zama kalubale ga mutanen da suka “binne haramtattun kudadensu a karkashin kasa.”

XS
SM
MD
LG