Faduwar darajar Naira a wannan karo ya shafi canjin gwamnati da na kasuwar bayan fage da hakan bai faye zuwa a lokaci daya ba.
Wannan lamari abun lura ya tabbata a karshen makon nan inda dala a canjin hukuma ta haura Naira 444 inda a kasuwar canjin a ke sayen ta kan Naira 778 a kuma sayar kan Naira 783.
Hakan na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnan babban banki Godwin Emefiele ya yi cewa bankin na shirin sauya takardun Naira zuwa sabon samfur daga tsakiyar watan gobe.
Wannan mataki a siyasance inji masanin siyasa na jami’ar Abuja Dr.Abubakar Kari ba zai gyaru ba sai in masu zabe sun yi tsayin daka wajen dora wadanda ke da kishin raya tattalin arziki kan madafun iko a 2023.
Shi kuma masanin tattalin arziki Yusha’u Aliyu ya cigaba da nanata dalilan da kan sa matakan sauko da darajar dala ba sa tasiri don yanda kusan kacokan Najeriya ta dogara ga dalar wajen sayo hajoji daga ketare.
Tuni a ka yi hasashe mai tada hankali cewa zuwa karshen shekarar nan dala za ta iya kai wa har Naira 1000.
Saurari rahoton cikin sauti: