Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Kungiyar MIYETTI ALLAH Ya Bar Baya Da Kura


Baba Usman Ngelzarma ya zama sabon shugaban MIYETTI ALLAH
Baba Usman Ngelzarma ya zama sabon shugaban MIYETTI ALLAH

Zaben sabbin shugabannin uwar kungiyar Fulani makiyaya ta “MIYETTI ALLAH” ya bar baya da kura don daya daga ‘yan takara ya ce bai amince da sakamakon zaben ba.

Miyetti Allah ce kan gaba da kuma tafi dadewa a tsakanin kungiyoyin makiyaya a Najeriya kuma ta na karkashin jagorancin Sarkin Musulmi Sultan na Sokoto.

Bayan kammala wa’adin tsohon shugaban kungiyar Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru an shirya zabe inda tsohon sakataren kungiyar Baba Usman Ngelzarma ya zama sabon shugaba.

A wani taro bayan zaben Baba Ngelzarma ya nemi hadin kan dukkan makiyayan da alwashin yin duk mai yiwuwa wajen yi musu jagoranci nagari kasancewar sa ba bako ba ne a jagorancin kungiyar.

Daya daga ‘yan takarar Sa’idu Maikano ya yi watsi da sakamakon zaben, ya na mai cewa an dawo da wadanda a ka zubar a wajen tantancewa cikin zaben.

Maikano ya bukaci a soke zaben da kafa shugabannin rikwan kwarya.

Za a jira a ga yanda iyayen kungiyar za su shawo kan wannan kura don karfafa hadin kai a lokacin da makiyaya da ke daji su ke korafin barayin daji sun hana su sakat kuma jagororin birni ba sa kai mu su dauki.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG