Otom na ganawa da tawagar gwamnoni biyar ne da su ka yi wa jam’iyyar PDP bara’a kan shugaban jam’iyyar Iyorchia Ayu ya sauka daga mulki don shugabancin ya koma kudu.
Gwamna Otom wanda dama ya saba furta irin wadannan kalamai na kabilanci, ya ce ya san ko yaya, za a yi ma sa fassarar da ba lalle haka ya ke nufi ba, don haka ya na ba da hakuri.
Otom a taron kaddamar da kamfen a Makurdi gaban gwamnonin PDP na bara’a, ya ce duk wanda ya marawa Atiku baya makiyin jihar Binuwai ne kuma shi sam ba zai zabi Bafulatani ba don zargin da ya ke yi cewa Fulani ke kashe al’ummar jihar sa.
Otom ya ce zai juyo kan ‘yan majalisar dokokin tarayya da ke hada kai da shugaba Buhari wajen zubar da jinin mutanen Binuwai.
“Da in zama bawan Fulani gara na mutu ma” inji Otom.
Tafiyar gwamnonin biyar na karkashin gwamna Nyesom Wike na Ribas ne wanda tuni ya janye goyon bayan sa ga dan takarar jam’iyyar Atiku Abubakar.
Gwamnonin biyar in ban da Seyi Makinde na Oyo da bai samu shiga Bauchi ba, sun gana da gwamna Bala ne don kokarin shigar da shi tafiyar su ta yi wa PDP tawaye.
Masanin kimiyyar siyasa Dr.Abubakar Kari ya ce har yanzu ba a rabu da Bukar kan siyasar kabilanci da makamantan su a zaben Najeriya ba.
Gwamna Bala dai shi ma ya rubuta takardar korafi ga PDP cewa ya gano wasu a jam’iyyar na shirya ma sa makarkashiyar hana sake zaben sa karo na biyu.
Akalla dai an sulhunta da gwamna Bala inda a ka gan shi ya dauki hoto da Atiku Abubakar.
Ga sautin rahoton Nasiru Adamu El Hikaya daga Abuja: