Shirin na wannan makon na tattaunawa ne akan bukatar kafa cibiyoyin kudi a Arewa da sauran hanyoyin raya arziki musamman a yankunan karkara.
A cikin shirin na wannan makon, mun duba batun kawo shawara ce ta kafa bankuna mallakar yankin Arewa da rassa a dukkan Jihohin Arewa 19 don matso da bankuna kusa da jama’a musamman mazauna karkara.
Kwana daya gabanin gudanar da gangamin yakin neman zabe na jam’iyyar PDP a jihar Ribas, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar ya janye kamfen din don abin da a ka zaiyana da gudun asarar rayuka.
A cikin shirin na wannan makon, mun duba batun bunkasa harkokin ilimi a yankin Arewacin Najeriya, inda yara kanana da dama ba sa zuwa makaranta ko kuma su na gararamba kan tituna ba tare da samun kulawar da ta dace daga gwamnatoci da kuma iyaye ba.
Tawagar masu ziyara daga Najeriya zuwa birnin Kaulaha a Senegal da su ka tsallake rijiya da baya a kisan gillar da jami’an tsaro su ka yi musu a Burkina Faso sun isa Kaulaha.
Kungiyar Ansarul Din Attijjaniyya da ke zama uwar kungiyoyin darikar Tijjaniyya ta yi Allah wadai ba bude wuta kan wata tawagar 'ya'yanta daga Najeriya da sojoji suka yi a Burkina Faso a kan hanyarsu ta zuwa birnin Kaulaha na kasar Senegal.
A cikin shirin na wannan makon, mun duba muhimmancin kafa tasoshn sauke hajar teku a tudu a yankin Arewacin Najeriya da ba ya kusa da gabar teku.
Karin kwana goma da babban bankin Najeriya ya yi don canja tsoffin kudi ya rage zullumin jama'a da ke fafutukar yin canjin.
Dan takarar Shugaban kasa na NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya ce ba wanda zai yi asarar kudin sa matukar ya hau karagar mulki.
A cikin shirin na wannan makon, bangare ne na karshe da ya duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar marabtar baki, kyautata makwabta, tallafawa marayu da sauran su.
Masana na baiyana cewa sai ‘yan Najeriya a dukkan sassa sun yi zabe nagari ba da la’akari da wani bambanci ba ne za a iya samun cin gajiyar arzikin kasar mai yawa.
Najeriya ta samu nasarar yin taro da hukumomin aikin hajji na Saudiyya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da aikin hajjin bana.
Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta bayyana cewa, ba a fahimci kalaman jami’inta mai kula da cibiyar horarwa kan zabe bane, wato Farfesa Abdullahi Zuru, akan fargabar da ake fuskanta game da zaben.
A cikin shirin na wannan makon mun ci gaba ne da wanda mu ka fara a makon jiya da ya duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar marabtar baki, kyautata makwabtaka, tallafawa marayu da sauran su.
Babban bankin Najeriya CBN na kan bakan sa na dakatar da aiki da tsoffin kudi a karshen watan nan duk da bukatar tsawaita lokacin daga majalisar dattawa.
Domin Kari