Shugaban hukumar INEC Farfesa Mahamud Yakubu ya bayyana kwarin gwiwa game da babban zaben, abin da ya kara rage fargabar dage zabe kamar yadda ya faru a shekarar 2015 da 2019.
“Asabar din nan ta ke ranar babban zabe, don haka kowa ya fita yin zabe. Za a bude rumfunan zabe daga karfe takwas da rabi na safe a rufe da karfe biyu da rabi na rana, a cewar shugaban na INEC a wani taron manema labarai, ya kuma ce ko bayan karfe biyun duk wanda ya ke kan layi zai samu damar kada kuri’arsa.
Farfesa Yakubu ya kara da cewa hukumar ta samu bayanin janyewar wasu jami’an wucin gadi da ke yi wa kasa hidima su kusan 100 daga aikin zaben a yankin Okigwe da Orlu a jihar Imo saboda dalilan tsaro, amma duk da haka za a gudanar da zabe a yankunan bisa tabbacin hukumomin tsaro.
Wani muhimmin labari a kan zaben shi ne dage zaben majalisar dattawa a mazabar Enugu ta gabas saboda kisan gillar da aka yi wa dan takarar jam’iyyar Labour Chukwu Oyibe. A saboda haka aka ba jam’iyyar dama ta sake zaben fidda gwani wanda za a yi da na gwamnoni da 'yan majalisar jiha a ranar 11 ga watan Maris.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, a ta bakin babban Sufeta Usman Baba Alkali, ta ce ta tura jami’an ‘yan sanda 428,000 don sa ido a zaben, shi ya sa ake karfafa jama'a su fita yin zabe ba tare da wata shakka ba.
Jam’iyyu 18 ne su ka tsayar da ‘yan takara, amma masu sharhi sun fi maida hankali kan ‘yan takara 4 daga jam’iyyun APC, PDP, Labour da NNPP.