Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa za ta tabbatar an gudanar da zaben 2023 cikin adalci inda za a damka ragama ga wanda mutane su ka zaba.
A cikin shirin na wannan makon mun duba yadda tarihin yankin Arewa ya ke a baya, inda mutane kan taimakawa juna ta hanyar karbar baki, kyautata wa makwabta, tallafawa marayu da sauran su.
Dan takarar jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya musanta labarin da ke cewa ya gana da wasu gwamnoni su 5 da su ka yi wa PDP a London.
Masu sha'awar kwallon kafa da ma sauran jama'a a fadin duniya na ci gaba da nuna alhini kan rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil , Pele.
A cikin shirin na wannan makon bita ce ta karshe ta shirin a shekara ta 2022 mai bankwan, mun duba koyar da matan Fulani makiyaya da ke zama a dazuka sana'o'i don samun dogaro da kai ko da wani dalili zai sa su rasa shanun su.
Wani lauya a Abuja, Barista Mainasara Kogo Umar, ya bayyana cewa shekara ta 2022 mai bankwana na daga cikin shekarun da ‘yan Najeriya ba su samu wani canji mai ma’ana ba.
‘Yan takarar mukamai daban-daban a zaben 2023 na jan hankalin magoya baya wajen ambata alkawuran canji da za su kawo in an ba su dama.
Shirin ya duba abubuwan da su ka karkace da in an saita su, yankin arewa ka iya farfadowa daga matsalolin da ya shiga da ba a yi tsammanin su ba a tarihin baya.
A cigaba da yakin neman zaben sabon shugaban Najeriya a ranar 25 ga watan Febrairu mai zuwa, ‘yan takarar manyan jam’iyyu da magoya bayan su na bayanan abubuwan da a ke ganin za su haddasa mu su cikas.
Wani kwamitin bincike na mutum 7 da shugaba Buhari ya kafa a asirce don duba ayyukan tara kudaden shiga na yau da kullum na bankuna, ya gano zunzurutun kudi da su ka kai dala biliyan 171 da babban bankin Najeriya ya ajiye a wani asusun da baya amfanar gwamnati.
Hukumar kwastam ta Najeriya ta bayyana cewa yakin Ukraine ya kawo koma baya wajen kammala tara kudin shiga da gwamnati ke son hukumar ta tara da su ka kai Naira tiriliyan 3.1.
Hukumar kwastam ta ce a fili ta ke gudanar da gwanjan kaya kuma kowa zai iya shiga yanar gizo ya ga yanda a ke gudanar da cinikin.
Kungiyar ta Miyetti Allah, ita ce uwar kungiyar da ke kula da alma'muran mafi aksarin Fulanin Najeriya wadanda suke zaune a sassan kasar.
Domin Kari