Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Wanda Zai Yi Asarar Kudinsa Idan Na Hau Mulki – Kwankwaso


Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso

Dan takarar Shugaban kasa na NNPP, Rabi'u Kwankwaso, ya ce ba wanda zai yi asarar kudin sa matukar ya hau karagar mulki.

Kwankwaso wanda ya bukaci gwamnati ta sauya matsaya kan batun canjin, ya ce rashin yin hakan zai jefa Najeriya cikin babban kalubale.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke korafin tuni wasu sun daina karbar kudin gabanin wa'adin karshen watan nan.

Rabi'u Kwankwaso ya ce yana takaicin yadda babban bankin ya ki amincewa da hatta kiran majalisar dokoki na kara wa'adin canjin.

Rahotanni na nuna a sassan Najeriya wasu kasuwanni sun dakatar da

Yanzu dai za a jira a ga ko babban bankin zai saurari barazanar Majalisa ta sa kafar wando daya da Emefiele.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-hikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

XS
SM
MD
LG