Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZAUREN MATASA: Matasa Sun Bada Shawarwari Don Ganin An Inganta Tsaro a Jihar Sokoto, Kashi Na Uku, Fabrairu 05, 2023


Nasiru Adamu
Nasiru Adamu

ABUJA, NIGERIA - Shirin na wannan makon ya ci gaba da tattaunawa da matasa a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya kan batun kalubalen tsaro da ke addabar wasu kananan hukumomin jihar.

Matasa a zauren sun bada shawarwari kan hanyoyin samun maslaha da kuma bukatar ‘yan siyasa su gujewa amfani da matasan wajen zama ‘yan banga, maimakon hakan su ja matasan a kusa, tare da sanya su bisa mukaman jagoranci don bada ta su gudummowar wajen raya kasa.

Kishin kasa da cusa kyawawan dabi’u na daga abubuwan da matasan su ka karfafa a zauren.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

ZAUREN MATASA: Matasa Sun Bada Shawarwari Don Ganin An Inganta Tsaro a Jihar Sokoto, Kashi Na Uku: Fabrairu 05, 2023
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:32 0:00

XS
SM
MD
LG