Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ba da tabbacin kammala dukkan shirye-shirye don gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisar jiha a jihohi 28 na kasar ranar Asabar 18 ga watan Maris.
Hukumar zaben Najeriya INEC ta ba da kwarin gwiwar shawo kan dukkan matsalolin da ta samu da aiki da na’urar tantance masu kada kuri’a BVAS a ranar Asabar din nan yayin da za a gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha.
A cikin shirin na wannan makon, mun duba batun sake karfafa bukatar farfado da ginshikan kyawawan dabi'u na al'ummar arewacin Najeriya daga kaka da kakanni.
Duk da ba lalle ba ne gwamnoni da ke mulki su lashe zabe karo na biyu, amma kwarin guiwar ‘yan hamaiya ya fi karfi a jihohin da gwamnaonin za su kammala wa’adi a ranar 29 ga watan mayu mai zuwa.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta na nan ta na kokarin ceto mutanen da a ka sace a yankin Biaji na babban birnin tarayya Abuja.
Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta dage gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisar jiha zuwa ranar Asabar 18 ga watan Maris.
A cikin shirin na wannan makon mun duba batun yunkurin wayar da kan jama’a kan illar tsattsauran ra’ayi da wasu kan fada ciki daga yankin Arewacin Najeriya mai iyaka da yankunan Sahara na Yammacin Afirka.
Majalisar kwamitin kawancen arewa NORTHERN ALLIANCE COMMITTEE ta ce don nuna tsarin adalcin arewa da bukatun zaman tare a Najeriya ya sa su ka mara wa Bola Tinubu baya a zaben da ya gabata.
Tawagar dan takarar jam’iyyar PDP a babban zaben 2023 Atiku Abubakar, ta gudanar da zanga-zangar lumana zuwa hukumar zabe don nuna rashin amincewa da sakamakon zaben.
Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen matasa a arewacin kasar ta bukaci duk mabiya su kwantar da hankalin su biyo bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya.
Kotun daukaka kara ta bai wa dan takarar jam'iyyar PDP Atiku Abubakar da na jam'iyyar Labour Peter Obi hurumin hukumar zabe ta ba su dama su binciki kayan da a ka yi amfani da su wajen gudanar da babban zaben 2023.
Shugaban hukumar zaben Najeriya INEC Farfesa Mahmood Yakubu ta mika shaidar lashe zabe ga zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
A cikin shirin na wannan makon mun duba dukiyar Arewacin Najeriya kamar ma’dinai, noma da kiwo da sauran su.
Yayin da wasu wakilan jam’iyyun adawa su ka marawa PDP da Leba wajen ficewa daga dakin tattara sakamakon zaben shugaban Najeriya, wasu bangaren na ‘yan adawa sun kara gyara zama ne da nuna sun yi na’am da yanda sakamakon ke fitowa.
Wasu 'yan adawa sun fice daga dakin gabatarwa da sanar da sakamakon zaben shugaban Njaeriya, don rashin gamsuwa ga yadda a ke gabatar da sakamakon.
Wakilan jam'iyyun hamaiya sun yi watsi da yadda a ke gabatar da sakamakon zaben shugaban Najeriya a wuni na biyu da fara gabatar da sakamakon.
Hukumar zaben Najeriya ta karbi sakamakon zaben shugaban kasa daga jihar Ekiti, wacce da ma ta kan zama ta farko a wajen tura sakamako.
Domin Kari