Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta gargadi masu mu’amula da kudade ta na’urar POS, akan su kiyaye ka’idojin mu’amula da kudade ko su dandana kudarsu.
A Najeriya mahukunta a jihar Sakkwato dake arewacin kasar na daukar matakan hana yaduwar wata cuta da ta bulla a makarantar ‘yan mata har ta yi sanadin salwantar rayuwa.
Al'ummomi a arewa maso yammacin Najeriya na ci gaba da zaman zulumi saboda rashin tabbas na tsaron rayukansu, duk da ikirarin da hukumomi ke yi na kokarin shawo kan matsalolin rashin tsaron.
A Najeriya kasancewar matakan da gwamnatoci ke cewa tana dauka na dakile ayukkan ta'addanci ba sa hana al’amarin gudana ba, al'umomi sun fara samun kwarin gwiwar yin fito-na-fito da 'yan ta'addar har da samun galaba.
Sabon Khalifar Tijjaniya ya bukaci mabiya darikar su dukufa da addu'a.
A Najeriya duk da fafatukar da hukumomi da kungiyoyin kare hakkin bil adama ke yi don saukaka matsalolin fyade, har yanzu ana ci gaba da fuskantar wadannan matsalolin a wasu sassan kasar.
Wata hatsaniya ce ta bulla a garin Yauri na jihar Kebbi dake Arewacin Najeriya tsakanin ‘yan sa kai da Fulani abin da yayi sanadiyar mutuwar mutum uku wasu suka samu raunuka.
À Najeriya tabarbarewar rashin tsaro har ya kai ga ‘yan ta’adda ke da iko da wasu kauyuka a wasu sassa na arewacin kasar.
Jamhuriyar Benin tana shirin kulla kawance da Najeriya a haujin noman shinkafa domin habbaka samarwa da dogaro da shinkafar da suka noma cikin gida ga kasashen biyu.
Daruruwan ‘yan bindiga sun yi dirar mikiya a garin Amarawa na yankin Illela ta gabashin Sakkwato inda suka hallaka mutane da dama kuma suka sace wani mutum.
An fara samun kwanciyar hankali bayan wata hatsaniya da ta barke tsakanin daliban jami'ar kimiya ta kere kere ta jihar Kebbi dake Aliero da kuma mutanen garin.
Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kaddamar da bincike akan wani mutum da aka kama da hodar cocaine da aka kiyasta kudinta ya kai naira biliyan daya.
Gwamnatin jihar Sokoto ta tasa keyar wasu magidanta bakwai zuwa gidan gyara hali, bayan da ta sake gurfanar da su gaban kotu akan zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 12 fyade.
A Najeriya matsalar rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara; abin da yasa al'ummomi ke ta yin kaura daga garuruwansu domin neman tsira, kamar yadda yake faruwa a jihar Kebbi da ke Arewacin kasar.
A daidai lokacin da wasu shugabannin al’umma ke daukar mataki ko kiran a samu da hanyar sasantawa da ‘yan bindiga domin samar da masalaha ga matsalar tsaro, shin ko ‘yan bindigar sun shirya ajiye makamansu?
A Najeriya sojojin bataliya ta daya dake garin Dukku a jihar Kebbi sun samu kwarin guiwar iya tunkarar matsalar rashin tsaro da ke son lalata zaman lafiyar da aka San jihar dashi tsawon shekaru masu yawa.
A ci gaba da lalaben mafita ga matsalolin rashin tsaro da malamin addinin nan Dr. Ahmad Gummi ya ke yi, ya hadu da shugabannin al'ummomi a Sakkwato inda suka tattauna hanyoyin samar da maslaha ga wadannan matsalolin.
A daidai lokacin da matsin lamba ke kara yawaita a kan fulani makiyaya su fice daga kudancin Najeriya, ‘yan arewa sun ce ai dama sakacin gwamnatoci ne ya kawo hakan domin arewa ta wuce ayi mata gori da fadin kasa mai dausayi da tsiro wadda kan iya wadatar da makiyaya.
Al'ummomi a Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren 'yan ta'adda duk da matakan da gwamnatoci ke cewa suna dauka.
Gwamnati jihar Sokoto ta dauki mataki akan wasu mutanen da ake zargi da yi wa wata yarinya fyade bayan kusan shekara guda da faruwar lamarin.
Domin Kari