Daidai lokacin da ya rage kwanaki kadan al'ummar Musulmin duniya su soma azumin watan Ramadan, shugaban majalisar koli akan lamurran addinin musulunci a Najeriya, mai alfarma sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar yana jaddada jan kunen jama'a akan abin da ya shafi duban wata domin kaucewa rabuwar kawuna da wasu lokuta ake samu akan ganin watan.
A Najeriya shugaban majalisar koli akan lamurran addinin musulunci ne shara'a ta baiwa iznin sanar da musulmi ganin watan musulunci wanda kuma aiki ne wanda da majalisar mai alfarma sarkin musulmi ke gudanarwa a kowane wata, a cewar shugaban kwamitin duban wata kuma Wazirin Sakkwato Farfesa Sambo Wali Junaidu.
Shi kansa mai alfarma sarkin musulmi a lokuta da dama yakan ja hankulan jama'a akan abin da ya shafi ganin wata, kamar lokacin wannan taro da ya yi da uwayen kasa 86.
Sai dai duk da haka wasu lokuta akan samu rabuwar kawuna akan farawa ko karewar watan Ramadan kamar yadda aka samu a shekarar bara ta 2020.
Shugaban kwamitin duban wata Farfesa Sambo Wali Junaidu yace jama'a fa su sani duban wata amana ce.
Yanzu da ya rage kwanakki kadan ga somawar Ramadan abinda kwamitocin duban wata sun bayyana fatar jama'a zasu aiki da umurnin da suka bayar domin kara samun hadin kai a Najeriya da ma duniya baki daya.
Saurare cikakken rahoton cikin sauti: