An kammala babban taron mabiya darikar Tijjaniyah na Afirka, tare da jaddada kira ga musulman duniya da su kasance masu kyawawan dabi'u, daidai da koyarwar addinin musulunci, domin samun salama da duniya baki daya.
Dubun dubatar magoya bayan darikar Tijjaniyah ne suka taru domin yin Maulidin Shehu Ibrahim Inyass Al kaulah.
Karin bayani akan: Sanusi Lamido Sanusi, Najeriya, da Najeriya.
Farfesa Abubakar Abubakar Yagawal, shi ne shugaban sufayen darikar ta Najeriya Yayi karin haske akan tarin bana, inda ya ke cewar, sun taron ne don tunatarwa da kuma kokarin yin koyi da koyarwar shehin nasu.
Malamai da suka fito daga kasashen duniya sun yi jawabai a lokacin wannan haduwar, Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daga cikin malaman.
Bayan addu'o'in zaman lafiya da aka gudanar wani babban abu da ya dauki hankalin taron na bana shi ne, sake kafa tarihi da tsohon sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya yi, wanda bayan gadon kakansa Sarki Sanusi na daya a zaman sarkin Kano, ya sake gadonsa a zaman Khalifan darikar Tijjaniyah na Najeriya.
Mukamin wanda ya rike shi na karshe shine marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u, sabon Khalifan na Tijjaniyah a Najeriya Sarki Sanusi na biyu ya yai jawabin cewa, jama'a su dukufa da yiwa kasa da shugabnni addu'a, da fatar Allah ya kawo dauki ga mabiya darikar bayan nadin nasa.
Wasu daga cikin mabiya darikar na bayyana fahimtar su akan sabon Khalifan. Suna fatar Allah ya bashi ikon jagoranci kamar yadda na baya suka yi.
Saboda cunkoson taron jama'ar da suka zo daga kasashen duniya, an samu afkawar rufin wata rumfa inda aka gudanar taron, har wasu bayanai sun tabbatar da an samu salwantar rayuwa daya yayin da wasu da dama suka jikkata.
Ga rahoton Muhammad Nasir a cikin sauti.