Ranar Talata ta wannan mako ne aka samu rahoton bullar wata cuta a daya daga cikin makarantun sakandaren ‘yan mata dake Sakkwato wadda ta kama dalibai da dama.
Dokta Abdulrahman Ahmad, daraktan kula da lafiyar al'umma, wanda a karkashin kulawarsa aka kai wa daliban dauki, ya bayyana muhimmancin daukar matakin.
Duk kokarin ganin daliban ya ci tura domin hukumar makarantar ta hana shiga makarantar sai dai bayanin da aka samu daga asibitin ya nuna adadin daliban da suka kamu zai kai kusan 50, to ko wane hali ake ciki yanzu?
Dokta Kulu Haruna Abubakar ita ce kwamishinar ilimin kimiya da fasahar kere kere wadda karkashin ta wannan makarantar take,
Wasu bayanai da aka samu daga asibitin sun tabbatar da cewa ba wannan makarantar ce kadai aka samu dalibai sun kamu da ciwo mai kama da annoba ba.
Akan haka ne masu sharhi kan lamurran yau da kullum, kamar Farfesa Bello Badah, ke ganin akwai bukatar hukuma ta kara kulawa musamman yanzu da yake an rufe wasu makarantu saboda matsalar rashin tsaro, aka hade dalibansu da makarantun da ke cikin gari don haka dole a samu cunkoso.
Yanzu gwamnatin ta ce tana gudanar da bincike domin gano kowace irin cuta ce da abinda ya haddasa kamuwa da ita domin kara daukar matakai na gaba.
Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun annoba ta amai da gudawa har a samu hasarar rayuka abin da hukumomi ke kula ga jama'a da su rika kulawa da tsabta.