Yawaitar samun matsalolin fyade ne ya zaburar da kungiyoyin kare hakkin bil'adama wajen jan hankalin hukumomi domin daukar matakan dakile munanan ayyukan, inda har wasu jihohi kamar jihar Kaduna da Kebbi suka bayyana sabbin dokoki na zartar da hukunce hukunce ga masu aikata dabi'ar yayin da wasu jihohi kamar, Sakkwato, har yanzu ana aiki a kan dokokin.
Sai dai kuma har yanzu ana ci gaba da samun wadannan matsalolin, wadanda a cewar wata lauya mai fafatukar tsaya wa wadanda ke fuskantar shari'a a kan cin zarafi, Barrister Rashida Muhammad, abin damuwa ne.
Duk da cewa matsalolin fyade da ke gaban kotuna suna jiran hukumci a Sakkwato, an sake yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai fyade, abin da har ya so ya gusar da hankalinta.
Mahaifiyar wannan yarinyar ta nemi a yi wa ‘yarta, wadda marainiya ce, adalci da yake batun yana gaban kuliya.
Wannan matsalar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin samar da dokokin hukunta masu aikata irin wannan laifin a Sakkwato karkashin jagorancin cibiyar tabbatar yin adalci ga kowa tare da tallafin spotlight.
Da yake tuni an gudanar da wanda ake tuhuma da yi wa rayinyar fyade gaban kuliya, jama'a na fatan ganin an yi wa yarinyar adalci.
Ga dai rahoton da Muhammad Nasir ya aiko mana da Sakkwato: