Yunkuri na baya bayan nan shi ne wanda malamin addinin Musulunci, Dakta Ahmad Gummi, ke yi na ziyartar rugagen Fulani da kuma matattarar ‘yan bindiga domin tattaunawa da su da zummar a samu maslaha ga matsalolin rashin tsaro.
Al’umomin wasu daga cikin wuraren da ake ganin akwai ‘yan bindigar sun tabbatar da cewa akwai su, kamar yadda mai sa ido a karamar hukumar Wurno, Mu'azu Shehu Kwargaba ya tabbatar a lokacin ziyarar neman sasanci da yan ta'adda a yankin. Wanda kuma ya bayar da shaidar cewa shi ma an kama shi a baya, inda ya kwashe kwanaki 34 a hannun wadanda suka yi garkuwa da shi.
Kwana guda bayan ziyarar Dakta Gumi yankin gabashin Sakkwato, masu satar mutane sun tare hanyar Marnona zuwa Isa, inda suka tare wasu matafiya daga Sakkwato zuwa Shinkafi da jihar Zamfara ta wannan hanyar suka sace mutane uku.
Wannan lamari abu ne dake nuna shakku akan ko ‘yan ta'addar sun shirye zaman tattaunawar, a daidai lokacin da Dakta Gumi ke ci gaba da da’awar ganin an sasanta duk da yake wasu na kalubalantar wannan yunkuri na sa.
Mai sharhi akan lamuran tsaro, Kaftin Yahaya J. Umar Mai Ritaya, ya ce sulhu sahihiyar hanya ce ta samar da zaman lafiya, amma akwai abubuwan da ya kamata a kula da su wurin yin sulhun. Inda ya ce tabbas sai an tabbatar da wadanda ake shirin yin sulhun, kuma da gaske su ke yi, sannan a samar da rubutacciyar yarjejeniya.
Haka zalika, ya kara da cewa yana da kyau a yi kokarin magance matsalolin da tun farko suka ingiza ‘yan bindigar fara garkuwa da mutane domin kudin fansa.
Ganin yadda shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sauya manyan hafsoshin tsaro hadi da matakan da hukumomi ke dauka, mai yiwuwa idan aka sauya salon tunkarar matsalolin rashin tsaron a iya samun sauki.
Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.