Wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan jihar ta fitar dauke da sa hannun Kakakinta, SP Bala Elkana ta ce, an bi sahun ‘yan bindigar ne bayan kiran gaggawa da suka samu jim kadan bayan kisan Gulak.
Jiragen ruwan na LST, akan yi amfani ne da su ne wajen dakon makaman yaki kamar tankuna da rokoki wadanda akan tsallaka da su daga wani yankin zuwa wani.
“Bari na yi gargadi, babu wani mahaluki ko wata kungiya da za ta rika irin wannan aika-aika, ta kuma yi tsammani za ta tafi salim-alim.” In ji shugaban na Najeriya.
Zamalek ta doke takwarorinta karawarta ta US Monastir ta kasar Tunusia da ci 76-63 a gasra wacce aka watsa ta kai tsaye a kasashe da yankuna 215 cikin harsuna 15.
Rahotanni da dama sun ce daliban da aka sace a makarantar wacce ta maza da mata ce sun kai 200.
Bayanai sun yi nunin da cewa, Gulak ya rasa ransa ne bayan da wasu 'yan bindiga suka harbe shi yayin da yake kan hanyarsa ta komawa Abuja daga birnin na Owerri.
An yi ta kai ruwa rana tsakanin kungiyoyin biyu wadanda dukansu daga gasar Premier ta Ingila suka fito.
Sanarawar ta Yerima ta kara da cewa, dakarun Najeriyar sun kora su har suka tabbatar babu wata karin barazana ga garin na Rann.
A ranar Alhamis, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nada Manjo-Janar Farouk Yahaya a matsayin sabon babban hafsan sojin kasar.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Janar Farouk Yahaya a matsayin wanda zai maye gurbin Laftar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama.
Manjo Janar Yahaya, ya rike mukamai da dama ciki har da Kwamandan rundunar tsaro ta Briged da kuma mukamin Darekta a kwalejin sojoji ta AFSC.
Kocin kungiyar Real Madrid, Zinedane Zidane a ranar Allhamis ya ajiye aikinsa bayan da yanke shawarar kawo karshen zamansa a kungiyar.
Wannan nasara na nufin, ‘yan wasan na Angola sun kai zagayen Semi-finals, yayin da Morocco ta fice a gasar ta BAL.
Daliban Kwalejin Kiwon Lafiya da Fasaha, da ke Ijero-Ekiti a ranar Laraba sun yi zanga-zanga bayan da abokan karantunsu su kimanin 100 suka suma sanadiyyar shakar wani sinadari.
Ita dai Man City ba ta taba lashe kofin gasar ba, hasali ma, wannan ne karon farko da ta taba kai wa wasan karshe a gasar ta UEFA yayin da Chelsea ta taba lashewa a 2012.
“Dalilin kenan ma da ya sa yake Sallar Juma’a a fadarsa, maimakon ya je Masallaci.” In ji Garba Shehu.
Gabanin wannan sauyi na baya-bayan nan, Najeriya ta sha bin tsaruka daban-daban wajen kayyade farashin dala, a wani mataki na kaucewa karya darajar naira.
Libya ta fada cikin rikicin siyasa, bayan hambarar da gwamnatin Moammar Ghaddafi a shekarar 2011, tun daga lokacin, kungiyoyi masu dauke da makamai ke ta ja-in-ja kan shugabancin kasar.
Ganawar na zuwa ne yayin da Najeriya ta fara makokin kwana uku da hutun kwana daya da aka ba dakarun kasar saboda rashin sojojin da aka yi.
Domin Kari