Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin samun nasara akan mayakan Boko Haram da suka yi yunkuri kai hari akan rundunar “Operation Hadin Kai” da ke garin Rann a jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Sanawar da sojojin kasar suka fitar dauke da sa hannun kakakinta, Birgediya Janar Mohammed Yerima ta ce, ‘yan ta’addan sun kai harin dauke da motoci masu bindigogi a garin na Ranna wanda ke karamar hukumar Kala Balge.
“’Yan ta’addan sun yi yunkuri kutsa kai a kofar garin, amma dakarun Najeriya wadanda suke cikin shiri, sun yi musu kofar rago, suka fatattake su, har suka tsere suka bar makamansu.”
Sanarawar ta Yerima ta kara da cewa, dakarun Najeriya sun kora su har suka tabbatar babu wata karin barazana ga garin na Rann.
Karin bayani akan: Janar Farouk Yahaya, Boko Haram, Nigeria, da Najeriya.
“Sojojin Najeriya sun yi nasarar lalata mota daya mai dauke da bindiga sun kuma kwato makamai da dama ciki har da bindigar da ake kakkabo jirgin sama, mashin gun biyu da bindiga kirar AK-47 guda 8.”
“Sannan an kashe mayakan Boko Haram goma.”
Rundunar sojin Najeriyar ta ce, wannan nasara na zuwa ne, sa’o’i bayan nada sabon babban hafsan sojin kasar.
A ranar Alhamis shugaban Najeriya ya nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin wanda ya maye gurbin marigayi Laftanar Janar Ibrahin Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jigrin sama a makon da ya gabata tare da wasu manyan sojoji 10.