Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ta Sayo Jirgin Yakin Ruwa Bayan Shekara 41


Jirgin ruwan da Najeriya za ta kaddamar.(Twitter/@BashirAhmaad)
Jirgin ruwan da Najeriya za ta kaddamar.(Twitter/@BashirAhmaad)

Jiragen ruwan na LST, akan yi amfani ne da su ne wajen dakon makaman yaki kamar tankuna da rokoki wadanda akan tsallaka da su daga wani yankin zuwa wani.

Rundunar sojin ruwa ta Najeriya, na shirin kaddamar da wani sabon jirgin yakin ruwa wanda za a yi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

A cewar mai baiwa Shugaba Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad, za a kaddamar da jirgin ne a wata mai Yuni.

“Za a kaddamar da shi ne a Sharjah na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a wata mai zuwa.”

Jirgin yana da tsawon mita 100 wanda zai rika daukan makaman yaki.

“Wannan babban ci gaba ne, lokaci na karshe da Najeriya ta kaddamar da irin wannan jirgi (wanda ake kira LST a takaice,) tun a 1979 – shekara 41 kenan.”

Jirgin ruwan na LST, akan yi amfani ne da shi wajen dakon makaman yaki kamar tankuna da rokoki wadanda akan tsallaka da su daga wani yankin zuwa wani.

Dadin dadawa, jiragen yakin sama kan iya sauka akansa.

A kwanan hukumomin Najeriyar sun bayyana cewa, sun yi cefanan wasu jirage yakin sama daga Amurka, wadanda su ma ake shirin kawo su nan ba da jimawa ba.

Najeriya na fama da matsalolin tsaro da suka hada da na Boko Haram a arewa maso gabashi da ‘yan fashin daji a arewaci maso yammaci, da kuma mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra a kudu maso gabashi.

XS
SM
MD
LG