Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sai Inda Karfinmu Ya Kare A Neman Wadanda Suka Kashe Gulak – Buhari


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari)
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari (Instagram/ Muhammadu Buhari)

“Bari na yi gargadi, babu wani mahaluki ko wata kungiya da za ta rika irin wannan aika-aika, ta kuma yi tsammani za ta tafi salim-alim.” In ji shugaban na Najeriya.

Fadar shugaban Najeriya ta mayar da martani da kakkausar murya dangane da kisan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa tsohon mai baiwa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan sha’anin siyasa.

A daren ranar Asabar wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka tare motar Ahmed Ali Gulak yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin tashin jirage a Owerri, babban birnin jihar Imo, suka harbe shi har lahira.

“Sai inda karfinmu ya kare wajen tabbatar da cewa an hukunta wadanda suka aikata wannan danyan aiki, inda za mu gurfanar da su a gaban kuliya.” Shugaba Muhammadu Buhari ya ce, kamar yadda mai ba shi shawara kan kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.

Karin bayani akan: Gulak, IPOB,​ Goodluck Jonathan, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A ‘yan watannin nan, yankin kudu maso gabashin Najeriya, musamman a jihar Imo, ya shiga kangin hare-haren ‘yan bindiga, wadanda suke far ma ofisoshin ‘yan sanda da sauran ma’aikatun gwamnati.

Akan daura alhakin hare-haren akan kungiyar IPOB da aka haramta, wacce ke fafutukar kafa kasar Biafra, zargin da kungiyar ta sha musantawa.

Amma hukumomi sun sha kafa hujjar cewa kungiyar na da hannu a hare-haren.

“Bari na yi gargadi, babu wani mahaluki ko wata kungiya da za ta rika irin wannan aika-aika, ta kuma yi tsammani za ta tafi salim-alim.” In ji shugaban na Najeriya.

Ko da yake, ya koma jam’iyyar APC a shekarar 2018, Gulak wanda dan asalin jihar Adamawa ne, ya taba zama mai bada shawara ga tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan wanda dan jam’iyyar adawa ta PDP ne.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Ikechukwu Eze ya fitar, Jonathan ya kwatanta Gulak a matsayin mutum mai “biyayya da yi wa kasa hidima” yana mai mika ta’aziyyarsa ga iyalansa.

“Na kadu matuka da wannan mutuwa ta Gulak,” Jonathan ya ce.

XS
SM
MD
LG