Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za Mu Mutunta Shawarar Da Zidane Ya Yankewa Kansa – Real Madrid


Zinedine Zidane speaks during press conference in Madrid, Spain, May 31, 2018
Zinedine Zidane speaks during press conference in Madrid, Spain, May 31, 2018

Kocin kungiyar Real Madrid, Zinedane Zidane a ranar Allhamis ya ajiye aikinsa bayan da yanke shawarar kawo karshen zamansa a kungiyar.

“Ya zama dole mu mutunta shawarar da ya yankewa kansa, muna kuma mika godiyarmu da irin kwarewarsa, himma da shaukin aiki da mu da ya nuna mana cikin shekarun da ya kwashe.” Madrid ta ce a wata sanarwa a ranar Alhamis.

Kungiyar ta kara da cewa, “ Zidane, na daya daga cikin jaruman Real Madrid, kuma tarihin da ya bari zai wuce abin da ya cimma a matsayinsa na koci da dan wasa a kungiyar.

Wani lokaci da 'yan wasan Real suke murnar lashe wasa da Villareal a bara
Wani lokaci da 'yan wasan Real suke murnar lashe wasa da Villareal a bara

Wasu majiyoyi sun fadawa ESPN cewa a ranar Laraba Zidane ya yanke shawarar ajiye aiki a kungiyar wacce ke buga wasa a gasar La Liga da ke kasar Spain.

A ranar Asabar Real ta buga wasanta na karshe da Villareal inda ta lallasa ta da ci 2-1, amma hakan bai ba ta damar ta wuce Atletico Madrid ba, wacce ta lallasa Real Valladolid da ci 2-1 ta lashe kofin gasar a bana.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG