Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Nada Manjo Janar Farouk Yahaya A Matsayin Sabon Babban Hafsan Sojin Najeriya


Manjo Janar Farouk Yahaya.
Manjo Janar Farouk Yahaya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Janar Farouk Yahaya a matsayin wanda zai maye gurbin Laftar Janar Ibrahim Attahiru, wanda ya rasu a hatsarin jirgin sama. 

Hedkwatar tsaron kasar ce ta bayyana wannan sabon nadi a ranar Alhamis, wanda ke dauke a cikin wata sanarwa da kakakinta Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya fitar

Gabanin nada shi a wannan mukami, Janar Yahaya shi ne kwamandan runduna ta 1, shi ne kuma kwamandan rundunar yaki da ayyukan ta’addanci a arewa maso gabashin Najeriya da aka wa lakabi da “Operation Hadin Kai.”

Nadin nasa na zuwa ne kasa da mako guda, bayan rasuwar marigayi Attahiru.

Janar Attahiru ya rasu a ranar Juma’a 21 ga watan Mayu, tare da wasu sojoji 10 yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Jirgin ya fadi ne a kusa da filin tashin jirage na kasa da kasa da ke Kaduna.

An yi jana’izarsu a ranar Asabar 22 ga watan Mayu, a makabartar dakarun kasar da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

Wannan shi ne karo na uku cikin wa’adin mulkinsa na farko da na biyu, da Shugaba Buhari yake nada babban hafsan sojin kasa na Najeriya.

Karin bayani akan: Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, Abubakar Shekau, Boko Haram, Janar Attahiru, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

A baya ya nada Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai daga watan Yulin 2015 zuwa watan Janairun 2021- bayan da Buhari ya lashe zaben 2015.

Sai marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da aka nada daga watan Janairun 2021 zuwa 21 ga watan Mayu da ya rasu.

Mutuwar Attahiru na zuwa ne, a daidai lokacin da rahotanni ke cewa, an kashe shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ko kuma an jikkata shi, rahotannin da hukumomin Najeriyar ba su tabbatar ba.

Kalubalane da ke gaban sabon babban hafsan sojin kasar, kamar yadda masana a fannin tsaro ke fada, sun hada da yakin Boko Haram, matsalar masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji musamman arewacin Najeriya.

Baya ga haka, akwai matsalolin tsaro a kudanci, wadanda suka hada da masu fafutukar kafa kasar Biafra da ‘yan bindiga da ke kai hare-hare kan cibiyoyin jami’an tsaro musamman a kudu maso gabashi.

Wani abu da wasu suke ganin har ila yau zama kalubale ga Yahaya shi ne, irin shaidar da aka yi wa marigayi Janar Attahiru ta cewa ya dakko hanyar shawo kan rikicin Boko Haram - abin ka iya zama kalubale a idan ya gaza dorawa akan abin da ya marigayin ya faro.

XS
SM
MD
LG