Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce miliyoyin ‘yan Najeriya sun zaku su yi rijista da jam’iyyar yayin da take shirin fara aikin sabunta rijista ta yanar gizo a duk fadin kasar.
Mutanen kuma da ke fama da cutar a yanzu haka sun kai 9, 542 yayin da jimullar mutanen da cutar ta harba ya kai 177, 142 a cewar NCDC.
Baya ga mutum daya da ya mutu wasu mutum biyar sun jikkata wadanda aka kai su asibiti don samun kulawa.
Rundunar sojin Najeriya ta ce ana samun karin mayakan Boko Haram da na ISWAP da ke ajiye makamansu su mika wuya.
“FC Barcelona na mika godiyarta ga dan wasan bisa irin rawar da ya taka wajen dabbaka kungiyar, tana kuma masa fatan alheri a duk in da zai je.”
“Shi da kansa Kyari ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar 30 ga watan Yuni, jim kadan bayan ziyarar.”
An dai yi bikin karramawar ne a Zinder wanda yana daga cikin jerin shagulgulan da aka yi don murnar wannan rana ta samun ‘yancin kai.
A ‘yan kwanakin nan an yi ta rade-radin cewa Tinubu na fama da rashin lafiya a London.
Hukumomi a jihar sun ce ba a hada allurar riga-kafin Moderna da ta Astrazeneca suna masu cewa dole ne mutum ya tsaya akan guda daya.
“Allah ya sa Aljanna makomarki Hajiya, Allah ya jaddada rahama.” Alan Waka ya rubuta a shafinsa na Instagram.
Matakin ya biyo bayan tuhumar da Amurka take yi wa Kyari kan zargin ya karbi cin hanci a hannun wani dan Najeriya mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushppupi, zargin da ya musanta.
Sai dai kamar yadda doka ta tanada, Okagbare na dama ta nemi a sake yin gwaji a karo na biyu don a tabbatar da sahihancin sakamkon farko.
“’Rundunar 'yan sandan Najeriya na kara jaddada cewa ta himmatu wajen tabbatar da adalci da karfafa dangantakar da ke tsakaninta da FBI da sauran abokanan hulda na kasa da kasa.”
"Babu wani da ya nemi ko kwabo a hannun Abbas Huspuppi. Aikinmu ya karkakata ne kan ceto rayukan jama’ar da ake zargin ana yi wa rayuwarsu barazana.”
“Idan har akwai wani shiri makamancin hakan, gwamnati ba za ta tsaya tana wani taro a boye ba, dangane da wannan muhimmin batu da ya shafi rayuwar al’uma."
An dai yi ta yamadidin cewa jifan ta aka yi, amma jarumar ta bayyana akasin hakan.
A ranar 23 ga watan Yuli, wata kotun tarayya a Ikoyi, ta samu masu fashin teku da laifin satar wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa mai suna FV HAILUFENG II.
A kasafin kudin bana, Najeriya ta ware naira biliyan 742.5 cikin jumillar kasafin kudin kasar na naira triliyan 11.7, abin da ya yi daidai da kashi 6.3 cikin 100.
Tun a shekarar 2015 ake tsare da El Zakzaky da matarsa bayan wani sabanı da aka samu tsakanin mabiya kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Islamic Movement of Nigeria IMN da dakarun Najeriya.
Fadar shugaban kasar ta sha bayyana cewa Buhari kan je kasar waje don duba lafiyarsa tun ma kafin ya zama shugaban kasa.
Domin Kari