Shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya karrama gwamnan jihar Bornon Najeriya Farfesa Babagana Umara Zulum da lambar yabo ta biyu mafi girma a Nijar.
An karrama Farfesa Zulum da lambar yabo ta “de Grand Officer dans l’ Ordre,” wacce darajarta take daidai dai da ta GCON da ake bayarwa a Najeriya.
Hakan na faruwa ne yayin da Jamhuriyar ta Nijar take bikin cika shekara 61 da samun ‘yancin kai daga Faransa.
Wata sanarwa da shafin Facebook na gwamnan jihar Borno ya fitar, ta ce shugaba Bazoum ya karrama Zulum ne, saboda ya lura da irin yadda gwamnan “yake yaki da mayakan Boko Haram bisa gaskiya.”
“Da kuma yadda ya damu da halin da ‘yan gudun hijira ‘yan jihar Borno da ke samun mafaka a Nijar ke ciki, inda ya ziyarce su bila adadin tare da tallafa masu da kuma kokarin kwashe su su koma sabbin gidajen da aka gina masu a Borno.”
An dai yi bikin karramawar ne a Zinder wanda yana daga cikin jerin shagulgulan da aka yi don murnar wannan rana ta samun ‘yancin kai.
Wannan shi ne karo na farko da wani shugaban Jamhuriyar Nijar zai karrama gwamnan Najeriya da lambar yabo ta biyu mafi girma a kasar.
Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ta hada iyaka da wasu yankunan Nijar.
Dubban ‘yan gudun hijirar Najeriya ne suka tsere zuwa kasar Nijar don neman mafaka sanadiyyar rikicin Boko Haram wanda ya faro tun daga 2009.