Rundunar sojin ruwan Najeriya ta mika ‘yan fashin tekun nan 10 da aka yankewa hukuncin daurin shekara 12 ga gidan yarin Kirikiri.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar da yammacin ranar Laraba ta ce a ranar Talata aka mika mutanen ga gidan yarin wanda ke birnin Legas a kudu maso yammacin Najeriya.
A ranar 23 ga watan Yuli, wata kotun tarayya a Ikoyi, ta samu masu fashin teku da laifin satar wani jirgin ruwan ‘yan kasuwa mai suna FV HAILUFENG II.
Kotun har ila yau ta ci tarar kowannensu naira miliyan daya-
Yayin yanke hukuncin, Alkali Ayokunle Faji na kotun Ikoyi, ya ce harkar fashin teku na janyowa Najeriya abin kunya kana yana mummunan tasiri kan tattalin arzikin kasar.
“Ya kamata hukunci irin wannan ya zama ya yi daidai da laifin da suka aikata saboda ya zama izna ga wasu.” In ji wata sanarwa da rundunar sojin ruwan Najeriya ta fitar a ranar Juma’a dauke da sa hannun kakakinta Commodore Suleiman Dahun.
Yayin gabatar da bahasinsa, babban mai shigar da kara Mr. Labaran Magaji ya ce hukuncin zai zama darasi ga masu kwadayin aikata laifuka akan ruwayen Najeriya.
Idan za a iya tunawa a ranar 15 ga watan Mayun 2020, rundunar sojin ruwan Najeriya ta kubutar da fasinjojin jirgin ruwan na FV HAILUFENG II daga hannun ‘yan fashin teku.
Daga baya aka tuhumi mutum 10 da ake zargi da hannun a lamarin a gaban kotun tarayya da ke Ikoyi.
Masu kare mutanen da aka yanke wa hukunci sun ce za su daukaka kara.